AFIRKA
2 minti karatu
Burkina Faso da Mali da Nijar na neman hanyar zuwa teku ta Morocco bayan ficewa daga ECOWAS
Ƙasashen uku sun ce suna “faɗaɗa hanyoyinmu na [amfani da] teku " bayan sun fice daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) a shekarar da ta gabata.
Burkina Faso da Mali da Nijar na neman hanyar zuwa teku ta Morocco bayan ficewa daga ECOWAS
Sarki Mohammed VI tare da ministocin harkokin waje na ƙasashen Sahel a fadar masarautar da ke Rabat. / Others
29 Afrilu 2025

Ministocin harkokin waje na ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun bayyana a ranar Litinin cewa sun amince da tayin da aka yi musu na amfani da tashoshin jiragen ruwan ƙasar Maroko wurin kasuwanci da duniya, in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar Maroko.

Ministocin harkokin wajen ƙasashen sun bayyana matsayar ƙasashensu ne a lokacin da suke ganawa da Sarki Mohamed VI na Maroko a Rabat, in ji rahoton.

Ƙasashen na Yammacin Afirka, waɗanda ke ƙarƙashin jagorancin sojojin da suka ƙwace mulki, sun fita daga ƙungiyar ECOWAS ne a shekarar da ta gabata kuma suka ƙulla wani ƙawance na ƙasashen Sahel mai suna AES.

Maroko, wata muhimmiyar ƙasa mai zuba jari a fannonin kuɗi da noman Yammacin Afirka, ta bayyana shirinta na ba da damar hanyar kasuwanci [ta tashoshin jiragen ruwanta] a watan Nuwamban shekarar 2023, bayan ECOWAS ta ƙaƙaba takunkumin kasuwanci kan ƙasashen uku.

‘Faɗaɗa hanya’

Shirin na da sauƙin "faɗaɗa hanyarmu ta samun damar [amfani da] teku," kamar yadda ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop, ya shaida wa kafar watsa labaran gwamnati.

Ganawar "wani ɓangare ne na dangantaka mai tarihi da ƙarfi tsakanin Masauratar da ƙasashen uku na ‘yan’uwa da ke cikin ƙugiyar ƙasashen Sahel," in ji kamafnin dillancin labaran Maroko.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin ƙasashen AES da Aljeriya, kishiyar Maroko a yankin, ta yi tsami.

Aljeriya ta yanke dangantaka da Maroko kuma tana goyon bayan ƙungiyar Polisario Front mai neman ‘yancin Yammacin  Sahara, wani wuri da Maroko ke ganin nata ne kuma inda take gina wata tashar jirgin ruwa da kimarta ta kai dala biliyan ɗaya.

Korar dakarun Faransa

Sabuwar ƙungiyar AES ta kori dakarun Faransa da na ƙasashen yammacin duniya, kuma ta koma neman taimakin soji daga Rasha.

A watan Disamba, Maroko ta shiga tsakanin wajen tabbatar da sake jami’an leƙen asirin Faransa huɗu da aka riƙe a Burkina Faso, watanni biyar bayan Paris ta yarda da ikon Rabat kan yankin Yammacin Sahara.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us