AFIRKA
1 minti karatu
Ɗan ƙunar-baƙin-wake ya kashe mutum 11 a Mogadishu babban birnin Somalia
Mutumin ya tayar da bam ɗin ne a daidai lokacin da wasu matasa masu neman shiga aikin soja suka yi jerin-gwano a wajen wani sansanin soji a Mogadishu.
Ɗan ƙunar-baƙin-wake ya kashe mutum 11 a Mogadishu babban birnin Somalia
Kungiyar ta'addanci mai alaka da Al-Qaeda, al-Shabaab, ta ɗauki alhakin kai harin. / Reuters
18 Mayu 2025

Akalla mutum 11 sun rasa rayukansu yayin da wasu 20 suka jikkata bayan wani ɗan ƙunar-baƙin-wake ya tayar da bam a wajen wani sansanin soja a babban birnin Somaliya, Mogadishu, a ranar Lahadi, in ji wani jami'i.

Harin ya faru ne a sansanin sojojin Somaliya na Damaanyo da ke unguwar Hodan, inda aka kai wa matasa masu neman shiga aikin soja hari yayin da suke jerin-gwano a wajen ginin.

Wani jami'in tsaro daga unguwar Warta Nabada da ke kusa da wurin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa fararen hula biyu da wasu masu neman shiga aikin soja na daga cikin waɗanda suka mutu a harin. Ya ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci.

Kungiyar ta'addanci mai alaka da Al-Qaeda, al-Shabaab, ta ɗauki alhakin kai harin.

Al-Shabaab ta shafe fiye da shekara 16 tana yakar gwamnatin Somaliya, kuma sau da yawa tana kai hare-hare kan jami'an gwamnati da sojoji.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us