AFIRKA
4 minti karatu
Kotun MDD za ta yanke hukunci kan rikicin Gabon da Equatorial Guinea kan yankuna masu arzikin mai
Rikicin dai ya samo asali ne tun a shekarar 1900, lokacin da ƙasashen Faransa da Sifaniya da suka yi mulkin mallaka suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Pariskan da nufin samar da iyakokin ƙasashen biyu.
Kotun MDD za ta yanke hukunci kan rikicin Gabon da Equatorial Guinea kan yankuna masu arzikin mai
Kotun kasa da kasa ICJ ita ce babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya. / AFP / AP
19 Mayu 2025

A ranar Litinin ɗin nan ne ake sa ran babbar Kotun Majalisar Dinkin Duniya za ta yanke hukunci kan taƙaddamar da aka kwashe shekaru da dama ana yi tsakanin ƙasashen Gabon da Equatorial Guinea kan tsibirai uku na ruwa masu arzikin mai.

Ƙasashe biyu na yammacin Afirka sun yi ta cece-ku-ce a kan tsibirin Mbanie mai faɗin hekta 30 (acre 74) da wasu ƙananan tsibirai guda biyu, Cocotier da Conga, tun a farkon shekarun 1970.

Tsibiran ƙanana ne kuma kusan ba’a iya rayuwa a can, amma suna wani yanki mai arzikin mai da iskar gas.

Rikicin dai ya samo asali ne tun a shekara ta 1900, lokacin da ƙasashen Faransa da Sifaniya da suka yi musu mulkin mallaka suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya a birnin Pariskan da nufin samar da iyakokin kasashen biyu.

Sai dai Gabon ta yi imanin cewa yarjejeniyar da aka yi a baya ta Bata a 1974, a lokacin ta tabbatar da ikon mallakar tsibiran.

'Takarcen takarda'

Yarjejeniyar Bata ta "warware duk wasu batutuwan da suka shafi ikon mallakar tsibirai da kuma ƙayyade iyakoki", kamar yadda Marie-Madeleine Mborantsuo, Shugabar Kotun Tsarin Mulkin Gabon, ta shaida wa Kotun Ƙasa da Ƙasa ta ICJ a zaman da ta yi a watan Oktoba.

Ƙasar Equatorial Guinea ta ce Gabon ta mamaye tsibiran ne a shekarar 1972 kuma tun daga lokacin ta mamaye su ba bisa ƙa'ida ba.

Lauyoyin Equatorial Guinea sun yi watsi da yarjejeniyar Bata a zaman da aka yi a watan Oktoba, inda suka ce ba zato ba tsammani Gabon ta fitar da takardar a shekara ta 2003, abin da ya bai wa kowa mamaki.

"Babu wanda ya gani ko ya ji labarin wannan babban taron." kamar yadda Domingo Mba Esono, Mataimakin Ministan Ma'adinai da Sinadarin Hydrocarbons daga Equatorial Guinea, ya shaida wa alƙalan kotun ta ICJ.

“Bugu da kari, takardar da aka gabatar ba ta asali ba ce, sai dai kwafin da ba a tantance ba kawai,” in ji Esono.

Philippe Sands, lauya mai wakiltar Equatorial Guinea, ya yi watsi da Yarjejeniyar Bata a matsayin "tarkacen takarda".

'Ba a adana takarda da kyau ba'

"Ana rokon ku da ku yanke hukuncin cewa wata ƙasa za ta iya dogaro kan kwafin kwafin wata takarda da ake iƙirarin akwai ta, wacce ba za a iya samun ta ainihi ba, kuma wadda ba a ambace ta ba ko kuma wani abu da za a iya dogaro kanta a tsawon shekaru talatin," in ji Sands.

Tun a 2003 Equatorial Guinea take neman ainihin kwafin takardar yarjejeniyar Bata, kuma har ya zuwa yanzu ba ta yi nasara.

Mborantsuo ya yarda cewa "abin baƙin ciki shi ne, babu ɗaya daga cikin ɓangarorin biyu da zai iya samun ainihin daftarin takardar", lura da cewa an zana ta ne kafin zuwa kwamfutoci da sauran hanyoyin tattara bayanai.

"Ba a adana su yanda ya kamata ba saboda abubuwa da dama kamar - yanayi mara kyau, da rashin ƙwararrun ma'aikata da rashin fasaha," in ji Mborantsuo.

Ba kamar sauran ƙasashen da ke bayyana a gaban kotun ICJ da ke birnin Hague wadda ke shari’a kan taƙaddamar da ke tsakanin kasashe ba, Guinea da Equatorial Guinea sun amince da bukatar alƙalan kotun da su yanke hukunci a ƙoƙarin da ake yi na ganin an sasanta.

Ƙasashen biyu sun buƙaci kotun ta yanke hukunci kan wanne takardu ne za a yi aiki da su - yarjejeniyar Paris ta 1900 ko yarjejeniyar Bata ta 1974.

Kotun ICJ ba za ta yanke hukunci kan kasar da ya kamata a bai wa ikon mallakar tsibiran ba.

"Muna da yaƙinin hukuncin kotun zai taimaka wa ƙasashenmu wajen warware taƙaddamar da ke tsakaninsu kan batun haƙƙn mallaka da iyakoki, tare da samar da dawwamammen ginshiki wajen bunƙasa dangantakarsu," in ji Esono na Equatorial Guinea.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us