AFIRKA
1 minti karatu
Gwamnatin Nijar ta haramta hawa babura a wasu sassan yankin Dosso
Gwamnan yankin Dosso ya ce babban dalilin saka haramcin shi ne daƙile zirga-zirgar ‘yan ta’adda waɗanda suke amfani da babura domin sufuri.
Gwamnatin Nijar ta haramta hawa babura a wasu sassan yankin Dosso
Haramcin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun hare-hare na masu iƙirarin jihadi a wasu yankunan ƙasar. / Reuters
kwana ɗaya baya

Gwamnan yankin Dosso a Jamhuriyar Nijar, Kanal-Manjo Bana Alhassane ya ɗauki mataki mai tsauri a ranar Alhamis inda ya haramta hawa babura a wasu sassan jihar na tsawon watanni uku.

Gwamnan ya sanar da saka haramcin ne a ranar Alhamis, 15 ga watan Mayu inda a wasu sassan ya saka haramcin dindindin na tsawon wata uku, a wasu sassan kuma haramcin zai rinƙa aiki da dare.

Gwamnan na Dosso ya ce babban dalilin saka haramcin shi ne daƙile zirga-zirgar ‘yan ta’adda waɗanda suke amfani da babura domin sufuri.

Haramcin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun hare-hare na masu iƙirarin jihadi a wasu yankunan ƙasar.

Ko a Lahadin da ta gabata, sai da aka kashe sojojin Nijar da dama a wani harin ta’addanci, duk da cewa su ma sojojin sun kashe  gomman ‘yan ta’addan.

Mutanen da ke zama a karkara da dama sun dogara ne da amfani da babura domin gudanar da sufurinsu inda da wasu ke fargabar saka wannan doka, sai dai gwamnatin ta ce ya zama dole domin daƙile ayyukan ta’addanci.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us