AFIRKA
3 minti karatu
Ghana ta kama 'yan kasashen waje fiye da 2,000 da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba
Yawancin waɗanda aka kama a samamen sun fito ne daga Burkina Faso da ke maƙwabtaka, wadda ke ƙarƙashin mulkin soja, da kuma daga Togo. Wasu daga cikin su sun fito ne daga nesa kamar Najeriya.
Ghana ta kama 'yan kasashen waje fiye da 2,000 da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba
Shugaban Ghana John Mahama / Others
10 awanni baya

Jami'an shige da fice na Ghana sun ce sun tsare fiye da 'yan ƙasashen waje fiye da 2,000 da ba su da takardu a Accra ranar Juma'a, a wani aiki da nufin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma daƙile bara a kan tituna.

Daga cikin mutane 2,241 da aka kama a samamen na safiyar Juma’a, 1,332 yara ne, kamar yadda ma'aikatar shige da fice ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Ministan Cikin Gida, Muntaka Mubarak, ya bayyana a wani rubutu da ya wallafa a shafin Facebook cewa, “an gudanar da wannan aiki ne domin magance matsalar ƙaruwar bara da ake yi a kan tituna, da 'yan kasashen waje suke yi.

"Wannan abin yana haifar da barazana ga tsaron ƙasa, kuma yana ɓata sunan ƙasarmu," in ji shi.

Yawancin waɗanda aka kama sun shiga Ghana ta hanyoyi "waɗanda ba a amince da su ba, sun ƙetare muhimman wuraren shige da fice", a cewar sa.

Yawancin waɗanda aka kama a samamen sun fito ne daga ƙasar Burkina Faso da ke makwabtaka, wadda ke ƙarƙashin mulkin soji, da kuma daga Togo. Wasu daga cikin su kuma sun fito ne daga nesa kamar Najeriya.

Jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya za su tantance su kafin a mayar da su ƙasashensu na asali, inda hukumomi suka yi alƙawarin tafi lamarinsu cikin "cikakkiyar ƙwarewa, tare da mutunta haƙƙoƙinsu na ɗan’adam".

Wasu daga ‘yan ƙasar sun yi maraba da matakin.

John Gyamfi, wani ɗan Ghana mai shekaru 43, wanda ke sana’ar sayar da kayan gyaran motoci, ya ce kama mutanen da ake zargin sun aikata laifin "ya kamata a yi shi tun tuni".

"Wasu daga waɗannan ‘yan ƙasar wajen suna karuwanci da barace-barace,” a cewar sa.

"[Abin kunya ne: suna zuwa nan, mutane suna zaton 'yan Ghana ne, kuma suna kunyata ɓata sunan Ghana. Idan sun tafi, tituna za su sake tsafta,” in ji shi.

To sai dai wasu baƙin haure da ba su da takardu sun ce tsananin buƙata, ba aikata laifi ba ne ya sa suka isa Ghana.

"Samun abinci ya zame mana matsala," in ji Chamsiya Alhassan, wata uwa daga Nijar, kamar yadda ta shaida wa AFP yayin da take layi don shiga bas.

"An kashe mazajenmu da danginmu. Mun zo nan ne kawai don neman abin da za mu ci," kamar yadda ta ƙara da cewa.

Yankin Sahel na fama da ƙaruwar ta'addancin masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da Al-Qaeda da Daesh.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us