Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce an yi wa yara 266,218 allurar rigakafin ƙyanda a yankin Diffa inda adadin ya wuce na yaran da tun da farko aka ƙayyade za a yi wa - wato yara 241,610.
Kwamitin da ke sa ido kan gudanar da rigakafin wanda gwamnan yankin na Diffa Birgediya Janar Mahamadou Ibrahim Bagadoma ne ya bayyana wannan adadin, inda jami’an lafiya da sauran ƙawayen da ke bayar da tallafi suka halarci taron kwamitin.
Sun bayyana cewa an gudanar da rigakafin na cutar ƙyandar ga yara ‘yan wata shida zuwa wata 59.
A nasa jawabin, Gwamna Bagadoma ya bayyana godiyarsa ga dukkan mahalarta taron, inda ya jaddada muhimmancin wannan taro da aka yi domin nazarin ayyukan da aka yi a lokacin aikin rigakafin wanda aka gudanar tun daga ranar 18 zuwa 24 ga Afrilun 2025 a gundumomi shida.
"Ƙyanda ta kasance ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke haifar da mace-mace na ƙananan yara, musamman a Afirka, duk da cewa akwai maganin rigakafi mai inganci kuma maras tsada," in ji Janar Bagadoma, wanda a cewarsa aikin da ake yi na rigakafin wani ɓangare ne na aiwatar da shirin na shugaban ƙasa Janar Abdourahamane Tiani.
Bisa alƙalumman da aka bayar, an lura cewa cutar ƙyanda ta kasance babbar matsalar da ke damun al'umma a Nijar. Tsakanin 2012 da 2024, an samu rahoton ɓullar cutar. Misali, a cikin 2020, an samu rahoton ɓullar cutar kyanda 2,298, da kuma mutuwar mutane 13. Wannan adadi ya haura zuwa 10,635 da mutuwar 30 yayin binciken da aka gudanar bayan rigakafi tsakanin 2019 zuwa 2022.