Shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Sudan Abdel Fattah Al-Burhan ya naɗa Dafallah Al-Haj Ali a matsayin firaminista na riƙon ƙwarya kuma ministan majalisar gudanarwa ta ƙasar.
Al-Burhan ya bayyana haka ne a sanarwar da gwamnatinsa ta fitar ranar Laraba da maraice.
A halin yanzu Al-Haj shi ne jakadan Sudan a ƙasar Saudiyya kuma tun a shekarar 1980 yake aiki a Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar.
Ya riƙe muƙamin jakadan Sudan a Pakistan, Fadar Vatican da Faransa, sannan shi ne wakilin dindindin na ƙasarsa a Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai wato Organization of Islamic Cooperation (OIC) da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ba a naɗa kowa a matsayin firaminsta ba tun bayan da tsohon firaminista Abdalla Hamdok ya sauka daga kan muƙamin a watan Janairu na shekarar 2022 bayan juyin mulkin da Al-Burhan ya jagoranta a watan Oktoba na 2021.
Kazalika Al-Burhan ya naɗa fitaccen jami’in diflomasiyya Omer Mohamed Ahmed Siddiq a matsayin ministan harkokin wajen Sudan da Dr. al-Tahami al-Zein Hajar Mohamed a matsayin Ministan Ma’aikatar Ilimi.