Dakarun RSF na Sudan sun shafe kwanaki biyar a jere suna kai hare-hare a gabashi da kudancin Sudan ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa inda suka ƙara kai wani harin a ranar Alhamis, kamar yadda wata majiyar soji ta bayyana.
RSF ta kai sabon harin ne a babban sansanin sojin ruwa da ke wajen Port Sudan, da kuma wasu daga cikin defo-defo na fetur a kudancin birnin Kosti, kamar yadda wata majiyar soji da ta buƙaci a sakaya sunanta ta bayyana.
“Mayaƙan sun ƙaddamar da wani harin jirgi maras matuƙi a sansanin sojin ruwa na Flamingo da ke arewacin Port Sudan,” kamar yadda majiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP, inda yake nufin rundunar RSF da mayaƙa, waɗanda ke rikici da sojojin na Sudan tun daga Afrilun 2023.
An ji ƙarar fashewar abubuwa daga sansanin sojin ruwan bayan kai harin, kamar yadda majiyar ta ƙara da cewa.
Birnin Port Sudan wanda yake gaɓar Tekun Bahar Maliya, ya kasance wuri mai aminci tun bayan fara yaƙin Sudan inda ya karɓi dubban ‘yan gudun hijira da kuma samar da ofisoshin Majalisar Ɗinkin Duniya, sai dai zuwa ranar Lahadi lamarin ya sauya inda RSF bayan ta soma kai har can.
Tasiri kan ayyukan jinƙai
Birnin mai tashar jirgin ruwa ya kasance mashigar kayayyakin agaji cikin Sudan, haka kuma Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi gargaɗin cewa hare-haren “na barazanar ƙara ayyukan neman jinƙai da kuma ƙara taɓarɓara ayyukan jinƙai a ƙasar”, kamar yadda mai magana da yawunsa Stephane Dujarric ya bayyana.
A kudanci, jirage marasa matuƙa na RSF sun kai hari kan defo-defo a birnin Kosti da ke Jihar White Nile da ke ƙarƙashin ikon sojojin ƙasar, lamarin da ya tayar da babbar gobara, in ji wata majiyar soji.