AFIRKA
2 minti karatu
Harin bama-baman dakarun RSF ya kashe fararen-hula da dama a biranen Sudan – Soji
Rundunar sojin Sudan ta ce dakarunta sun yi nasarar daƙile harin da RSF ta kai El-Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, inda suka kashe 'yan ta'adda 600 tare da lalata motocin soji 25.
Harin bama-baman dakarun RSF ya kashe fararen-hula da dama a biranen Sudan – Soji
Sama da mutane 20,000 ne aka kashe ya zuwa yanzu, yayin da wasu miliyan 15 suka rasa matsugunansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin kasar / Reuters
kwana ɗaya baya

Aƙalla fararen-hula 41 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon luguden wuta da dakarun rundunar Rapid Support Forces (RSF) suka kai a El-Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, in ji rundunar sojin Sudan a ranar Talata.

Sanarwar da sojoji suka fitar ta ce mata da ƙananan yara na daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su a wasu unguwanni a birnin ranar Litinin da daddare.

Rundunar ta ce dakarunta sun yi nasarar daƙile harin da RSF ta kai birnin, inda suka kashe mayaƙan 600 tare da lalata motocin soji 25.

Kawo yanzu dai babu wani bayani ko martani daga ƙungiyar 'yan tawayen kan sanarwar da sojojin suka fitar.

Tun dai a ranar Litinin ake gwabza faɗa tsakanin dakarun soji da mayaƙan na RSF a garin El-Fasher, wanda ya tilasta wa gidajen abinci na agaji da ke birnin dakatar da rabon abinci ga fararen-hula.

Tun a watan Mayun 2024 ne El-Fasher ya gamu da ƙazamin faɗa tsakanin sojojin Sudan da RSF, duk da gargaɗin da ƙasashen duniya suka yi kan hatsarin faɗa a birnin, wanda ke zama cibiyar ayyukan jinƙai a dukkan jihohin Darfur biyar.

A farkon wannan watan, RSF ta yi iƙirarin cewa ta ƙwace iko da sansanin 'yan gudun hijira na Zamzam da ke birnin bayan arangama da dakarun soji. Aƙalla fararen-hula 400 ne aka kashe, kuma kusan 400,000 suka rasa matsugunansu sakamakon faɗan, kamar yadda alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya suka nuna.

Tun a ranar 15 ga Afrilu, 2023, RSF ke fafatawa da sojojin Sudan don samun iko a ƙasar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane da kuma ɗaya daga cikin mafi munin rikicin jinƙai a duniya.

Sama da mutane 20,000 ne aka kashe ya zuwa yanzu, yayin da wasu miliyan 15 suka rasa matsugunansu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin ƙasar.

Bincike daga ƙwararru a Amurka, ya ƙiyasta adadin waɗanda suka mutu ya kai kusan mutum 130,000.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us