AFIRKA
2 minti karatu
An kashe sojojin Nijar 12 kusa da iyakokin Mali da Burkina Faso
A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a harin.
An kashe sojojin Nijar 12 kusa da iyakokin Mali da Burkina Faso
Rundunar ta ce an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a harin. / Others
27 Afrilu 2025

Sojojin Nijar 12 aka kashe a wani hari da aka kai a yammacin ƙasar, kamar yadda wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta tabbatar.

Rundunar ta ce an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a harin.

An kai harin ne a ranar Juma’a a kusa da yankin da ke kan iyaka da Nijar da Burkina Faso da kuma Mali, inda wurin ya kasance wata cibiya ta tashe-tashen hankula a yammacin Afirka da al Qaeda da Daesh ake zargi da haddasawa.

Sanarwar ta ce, 'yan ta'adda ɗauke da makamai sun kai wani farmaki mai ban mamaki a kan rundunar soji da ke wani aiki a wani wuri mai nisan kilomita 10 daga arewacin ƙauyen Sakoira.

Sai dai ba a yi ƙarin haske kan ko su waye maharan ba amma a watan da ya gabata Nijar ta ɗora alhaki kan ƙungiyar ta’addanci ta EIGS mai alaƙa da Daesh bayan wani hari da aka kai kan wani masallaci da ke kusa da yankin iyakokin ƙasashen AES uku, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula aƙalla 44.

Rikicin Sahel dai ya samo asali ne daga tawayen Azbinawa a arewacin Mali a shekara ta 2012, daga bisani kuma ya bazu zuwa ƙasashen Burkina Faso da Nijar da ke maƙwabtaka inda daga baya ya ƙara bazuwa har arewacin ƙasashen yammacin Afirka da ke gaɓar teku kamar Benin.

An kashe dubban ɗaruruwan mutane yayin da wasu miliyoyi suka rasa muhallansu sakamakon harin da mayaƙan suka kai a ƙauyuka, ofisoshin sojoji da 'yan sanda da ayarin motocin sojoji.

Gazawar gwamnatoci wajen samar da tsaro ya taimaka wajen juyin mulki sau biyu a Mali, biyu a Burkina Faso da ɗaya a Nijar tsakanin 2020 zuwa 2023. Dukkanin ukun dai na ci gaba da zama karkashin mulkin soja.

MAJIYA:REUTERS
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us