Shugaban mulkin soja na Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore mutum ne da ke yawan jan hankalin jama’a a Afirka. Akwai matasa da dama da ke nuna masa soyayya inda suke kallonsa a matsayin shugaba mai kawo aƙidun kawo sauyi.
Ga wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani a kansa
Shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru
Kyaftin Ibrahim Traore shi ne shugaban ƙasa mafi ƙarancin shekaru a duniya, inda aka haife shi a ranar 14 ga watan Maris ɗin 1988. Shugaban Ecuador Daniel Noboa ya girme shi, da kusan watanni uku da rabi, sannan kuma Shugaban Kamaru wanda shi ne shugaba mafi tsufa a duniya ya girmi Traore da shekara 55.
Aikin soja
Traore dai ya shiga aikin sojan Burkina Faso ne a shekara ta 2009, ya kuma samu mukamin kyaftin a shekara ta 2020. Yana cikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali, daga bisani kuma ya yi yaki da masu tayar da ƙayar baya a ƙasarsa, inda ya samu yabo. Ya ƙwace mulki ne a wani juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Satumban 2022, inda suka hamɓarar da Kanal Paul-Henri Damiba.
Ƙungiyar Sahel Alliance
Tafiyar da Traore ya yi ta farko a matsayinsa na shugaban ƙasa ita ce tafiyar da ya yi zuwa Mali domin haɗuwa da Kanal Assimi Goita a ranar 2 ga watan Nuwamban 2022.
A halin yanzu Mali da Nijar su ne ƙawaye mafi kusa na Burkina Faso kuma ƙasashen sun haɗa kai inda suka samar da ƙungiyar AES wato Sahel Alliance bayan sun ɓalle daga ECOWAS.
Tafiye-tafiye ƙalilan
Ƙasar Afirkar da Traore kawai ya je wadda ba ta cikin AES ita ce Ghana, inda ya halarci bikin rantsar da Shugaba John Mahama a ranar 7 ga Janairun 2025.
Rayuwarsa ta sirri
Duk da cewa ana ganin shugabannin ƙasashe da dama tare da matansu da ‘ya’yansu a bainar jama’a, ga shugaban ɗan shekara 37, batun matarsa ko ‘ya’yansa ya kasance batu na sirri.