AFIRKA
2 minti karatu
Shirin WFP zai rage tallafin abinci a Sudan saboda katse zuwan kudade
Hukumar ta MDD ta ce tana fama da ƙarancin kuɗaɗe da suka kai dala miliyan 698 daga kusan dala miliyan 800 da ta buƙaci masu taimako su bayar don a agaza wa mutane miliyan bakwai daga watan Mayu zuwa Satumba.
Shirin WFP zai rage tallafin abinci a Sudan saboda katse zuwan kudade
Tallafin da aka bayar na abinci ya kawo raguwar yunwa da kasha 70 a yankunan da ke fuskantar hatsari, in ji WFP. / Rueters / Reuters
26 Afrilu 2025

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗi kan ƙarancin kuɗi da ka iya yin tasiri kan taimakon da yake baiwa mutanen da ke fuskantar ƙarancin abinci a Sudan, a cikin makonni, saboda dakatar da tallafi da masu taimako suka yi.

A ranar Juma’a, Hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tana fama da ƙarancin kuɗaɗe da suka kai dala miliyan 698 daga kusan dala miliyan 800 da ta buƙaci masu taimako su bayar don a agaza wa mutane miliyan bakwai daga watan Mayu zuwa Satumba.

Za a fuskanci ƙarancin kayayyaki irin su garin masara da hatsi da abinci haɗaɗɗe tun daga watan Mayu saboda a yanzu masu tallafi na ƙasa da ƙasa sun dakatar da bayar da tallafin.

Tallafin da ake samu na abinci a yankunan da ke haɗarin gamuwa da yunwa ya ragu da kashi 70, in ji WFP.

'Lokaci mai hatsari'

“Muna sake jaddada buƙatar tallafin kuɗaɗe a wannan lokaci mai hatsari inda muke shiga lokacin damina da kuma lokacin yunwa a Sudan, kuma a lokacin da rikici ke ƙara ta’azzara, ana samun karuwar tsugunar da jama’a,” kamar yadda Samantha Chattaraj, Jami’ar Jin Ƙai ta WFP a Sudan ta fada wa manema labarai.

A watan Afrilun 2023 ne rikici ya ɓarke a Sudan, saboda fafutukar iko tsakanin sojojin ƙasar da mayaƙan RSF. Rikicin ya raba miliyoyin mutane da matsugunansu.

WFP ta bayyana cewa tana ƙoƙarin neman taimako a faɗin kasar, ciki har da ma ga wasu mutane 450,000 da aka kora daga sansanin ZamZam a arewacin Darfur, bayan da mayaƙan RSF suka ƙwace iko da yankin a farkon wannan wata

Hukumar ta kuma ce ta taimaka wa mutane miliyan huɗu a faɗin Sudan a watan Maris - adadi mafi yawa a wata guda tun bayan fara rikicin - kuma a yanzu suna iya isa yankuna da dama, bayan magance ƙalubalen neman izini da na tsaro.

Ana sa ran zuwan ƙarin tirelolin kayan tallafi a ‘yan kwanaki masu zuwa.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us