Shugaban Kwamitin Mulki na Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya nada tsohon jami'in Majalisar Dinkin Duniya, Kamil El-Tayib Idris, a matsayin Firaminista.
Hukumar dillancin labarai ta kasa, SUNA, ta sanar a ranar Litinin cewa nadin Idris ya biyo bayan wata sanarwa da Burhan ya fitar, wanda shi ne kuma babban hafsan sojin kasar.
Idris tsohon jami'in Majalisar Dinkin Duniya ne kuma tsohon dan takarar shugaban kasa.
Nadin nasa ya kawo firaminista a karon farko tun watan Janairun 2022, lokacin da Abdalla Hamdok ya yi murabus sakamakon rikicin siyasa wanda daga baya ya rikide ya zama yakin basasa da har yanzu ke ci gaba da addabar kasar.
Kwamitin Mulki ya samu sabbin mambobi mata
A watan da ya gabata, Burhan ya nada wani gogagge a fannin diflomasiyya, Dafallah al-Haj, a matsayin mukaddashin firaminista.
Burhan ya kuma fitar da wata sanarwa inda ya nada mata biyu, Salma Al-Mubarak da Nawara Abu Mohamed Tahir, a matsayin mambobin Kwamitin Mulki, wanda hakan ya kara yawan mambobin kwamitin zuwa tara.
Tun daga watan Afrilun 2023, kungiyar sojojin sa kai ta Rapid Support Forces (RSF) ke gwabza fada da sojojin kasar don samun ikon mulkin Sudan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare da haifar da daya daga cikin mafi munin rikicin jinƙai a duniya.
Fiye da mutane 20,000 sun rasa rayukansu kuma an raba mutane miliyan 15 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin cikin gida.
Duk da haka, binciken wasu masana daga Amurka ya nuna cewa adadin wadanda suka mutu ya kai kimanin 130,000.