Hukumar Leken Asiri da Tsaro ta Somaliya NISA ta sanar da cewa dakarunta sun kashe Mohamed Abdi Dhiblaawe Afrax, wani babban kwamandan ƙungiyar Al-Shabaab, a wani samame da suka shirya yi a Ugunji, da ke yankin Lower Shabelle.
Hukumar ta NISA ta tabbatar da cewa Afrax ne ya shirya yunkurin kisan gillar da bai yi nasara ba a kan ayarin motocin Shugaban Ƙasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud a ranar 18 ga Maris ɗin 2025.
Harin 18 ga Maris na 2025
Da misalin ƙarfe 10:32 na safiyar ranar ne aka kai wa ayarin motocin shugaban hari a kusa da mahadar El-gaabta da ke gundumar Xamar-Jajab, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama domin tafiya tare da dakarun sa-kai na Hirshabesha.
Daya baya ma’aikatar yada labaran ƙasar ta tabbatar da cewa an daƙile harin, kuma shugaban ya isa inda ya yi niyyar zuwa.
Harin wanda ƙungiyar Al- Shabab ta ɗauki alhakin kai shi, ya janyo asarar rayukan fararen hula da suka hada da mace-mace da jikkata wasu.
Goyon bayan ƙasashen duniya
Harin ya jawo suka cikin gaggawa daga ƙasashen duniya, inda ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Larabawa ta bayyana shi a matsayin "tsantsar hari," yayin da Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmai (OIC) ta kira shi da "mummunan hari."
Kungiyoyin biyu dai sun jaddada cikakken goyon bayansu ga Somaliya a yakin da take yi da ta'addanci.
Hukumar ta NISA ta bayyana kisan Afrax a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da bin diddigin laifukan da ya aikata tare da yin alƙawarin fitar da ƙarin bayanai game da ayyukan ta’addancin da ya aikata nan gaba kadan.