An samu kari a Asusun adana zinare na Ghana zuwa tan 31.37 a watan Afrilun 2025, sama da tan 31.01 da aka samu a watan Maris kana sama da tan 8.78 a watan Mayun 2023.
Sabbin bayanai daga Bankin Ghana sun danganta wannan ci gaba da aka samu da karuwar sayen zinare da nufin karfafa asusun ajiyar waje da kuma bunkasa tattalin arziki.
Ta hanyar kara yawan hannayen jarinsa na Zinare, Babban bankin ya kuduri aniyar rage dogaro da kudaden waje da kuma karkata zuwa sauran albarkatun kasa.