Fadi-tashin Harry Kane kafin lashe kofin farko a rayuwarsa
WASANNI
5 minti karatu
Fadi-tashin Harry Kane kafin lashe kofin farko a rayuwarsaHarry Kane ya ci ƙwallo sama da 440 a rayuwarsa, amma tamkar wanda aka yi wa baki, bai taɓa lashe kofi ba sai a bana, a shekararsa ta biyu a Bayern Munich ta Jamus bayan ya baro Tottenham Hotspur ta Ingila.
/ AP
6 Mayu 2025

Ranar 4 ga Mayu ne Bayern Munich ta zama zakaran gasar Bundesliga, wadda ita ce babbar gasar ƙwallon ƙafa ta ƙwararru a Jamus. Wannan ne karo na 34 da ƙungiyar ta lashe kofin a tarihi.

Wannan nasara na nufin cewa ɗan wasan gaba na Bayern ya ci kofinsa na farko a rayuwarsa ta ƙwallo, kasancewa a baya bai taɓa bugawa ƙungiyar da ta lashe wani kofi tare da shi ba.

Harry Kane mai shekaru 31, shi ne kyaftin ɗin tawagar ƙasar Ingila, kuma haziƙin ɗan wasa ne da ya yi suna wajen cin ƙwallaye a ƙungiyoyin da ya buga wa wasa.

An daɗe ana yi wa Kane kallon ɗan wasa mara sa’a, kasancewar duk da ya haura shekaru 30 a duniya, kuma duk da buga ƙwallo tsawon sama da shekara 15 ajin ƙwararru, tun a 2009, bai taɓa cin wani kofi ba.

Sau da yawa akan ƙidaya Harry Kane cikin ‘yan ƙwallo mafiya gwaninta da jajircewa, amma waɗanda ba su da sa’ar cin kofin, wa lau a ƙungiyarsu ko a tawagar ƙasarsu.

Yawan ƙwallaye

Harry Kane ya ci ƙwallaye 447 a rayuwarsa, inda har ya ƙure masu sukarsa saboda ya taɓa zama wanda ya fi kowa cin ƙwallo a 2023-24 a duka gasannin ƙasashen Turai.

A kakar 2020–21 Kane ne ya fi kowa cin ƙwallaye (23), a gasar Firimiya inda ya kuma ba da tallafin (14). Ko a 2017–18, Kane ya ci ƙwallaye 41 cikin wasanni 48 a duka gasanni.

Sai dai duk da wannan tagomashi na ɗan wasan, bai samu nasarar lashe ko da ƙaramin kofi ba. A Tottenham, Kane ya je wasan ƙarshe na kofin Zakarun Turai, da wasan ƙarshe na kofin Carabao sau biyu.

A Agustan 2023, Harry Kane ya koma Bayern Munich kan euro miliyan 100, inda ake zaton cikin sauri zai samu damar lashe kofi a rayuwarsa, amma burin nasa ya gaza cika.

A ƙarshen kakarsa ta farko a Jamus, Bayer Leverkusen ce ta ɗaga kofin Bundesliga, sannan Bayern Munich ta gaza cin kowane kofi a gida da ma a nahiyar Turai.

Kwatanci da Gareth Bale

Kafin Harry kane ya bar Tottenham bayan ya yi shekaru 10 ba tare da ɗaga wani kofi ba, an yi ta kwatanta shi da wani tauraron ƙungiyar, wato Gareth Bale, wanda shi ma ya taɓa barin Tottenham don neman lashe babban kofi a wata ƙungiyar daban.

Bale ya bar Tottenham Hotspur yana da ƙaramin kofi ɗaya, na League Cup a Ingila. Amma a ƙungiyoyin Real Madrid ta Sifaniya da Los Angeles FC ta Amurka, Bale ya ci jimillar kofuna 19.

Ya ci babbar gasar Zakarun Turai 5, da kofin La Liga 3, da Copa del Rey 1, da Supercopa de España 3, da UEFA Super Cup 3, da kuma FIFA Club World Cup 3. Sannan ya ci kofin babbar gasar ƙwallon ƙafa ta maza a Amurka ta MLS Cup da Supporters Shield a 2022.

Wannan ya sa akan ce Harry Kane ya ɓata shekarunsa na samartaka a Tottenham, ya kuma saryar da damarmakin lashe kofuna lokacin ganiyarsa saboda cigaba da zama a can.

An taɓa ambato Harry Kane yana nuna takaicinsa na rashin ɗaga wani kofi, inda ya ce, "Burina ɗaya na lashe kofuna. Ba na jin akwai ranar da ke shuɗewa ba tare da na yi mafarkin lashe wata kyauta ba".

Barin Tottenham

Daga cikin dalilan da suka tilasta wa Kane barin Tottenham akwai lokacin da kulob ɗin ya sallami aƙaƙurin koci, Jose Mourinho, ‘yan kwanaki kafin buga wasan ƙarshe na gasar Carabao Cup.

Tottenham ta gaza cin kofin, kuma daga nan Kane ya ɗauki aniyar ƙaura daga Spurs, inda aka ruwaito cewa ya fara ƙauracewa atisaye don ya fusata kulob ɗin ya kore shi. Amma sai a ƙarshen kakar 2022-23 ne suka raba gari da Tottenham.

Kafin barin Tottenham, Kane ya kafa tarihin zama ɗan wasan da fi yawan ƙwallaye a tarihin ƙungiyar, da ƙwallaye 280 cikin wasanni 435 a duka gasanni, tarihin da aka yi shekara 50 kafin a kafa shi.

Harry Kane ya samu nasarar komawa kulub mafi girma da nasara a Jamus, wato Bayern Munich, inda ya bayyana farin cikinsa yana cewa, "A Spurs ina jin ko ƙwallo nawa na ci, matuƙar ban ci kofin Firimiya ko na Zakarun Turai ba, ba wanda zai kula ni. Na zo na 10 a ‘yan takarar Ballon d’Or a Spurs.

Lashe kofin farko

Sai dai a shekarar farko a Bayern, duk da ƙwallaye 44 da Harry Kane ya ci a wasanni 45, kofi bai samu zuwa hannunsa ba. Sai a bana ne Bayern ta ci kofin Bundesliga, inda ƙishirwar Kane ta zo ƙarshe.

Wannan nasara ta zama cikar burin wani ɗan wasa da ake yawan ambato cikin waɗanda suka wahala wa ƙwallon ƙafa ba tare da haƙarsu ta cim ma ruwa ba.

Wannan abin alfahari ne, saboda ko a tawagar Ingila ma, Kane bai samu damar taɓa kofi da hannunsa ba, cikin dukkan wasannin da tawagar Ingila ta Three Lions ta buga yayin da yake cikinta. Sau biyu Ingila na zuwa wasan ƙarshe na gasar ƙasashen Turai ta Euro.

A yanzu dai, nasara ta sa za a saka Harry Kane cikin taurarin ‘yan wasan ƙasar Ingila, kuma tuni aka saka shi cikin waɗanda suka cancanti lashe kyautar gwarzon ƙwallon ƙafa ta duniya, wato Ballon d‘Or a bana.

Zuwa yanzu dai, Kane ya buga jimillar wasanni 694, kuma ya ci ƙwallaye 447. Don haka ko da dai kofi ɗaya ya ci a rayuwarsa, za a iya cewa ɗaya ta fi babu, kuma sa’a ta tarar da rabo.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us