Yadda ma’aikatan jinya a Kenya, da Nijeriya da Mali ke gwagwarmayar ceton rayuka
AFIRKA
5 minti karatu
Yadda ma’aikatan jinya a Kenya, da Nijeriya da Mali ke gwagwarmayar ceton rayukaMa’aikatan jinya na Afirka na jure wa dukkan wahalhalu, suna aiki da ƙarancin kayayyaki, kuma ana tilasta musu yin zaɓi mai wahala a wajen aiki.
Ma’aikatan jinya a Afirka na baiwa marasa lafiya kulawa da kashi 43 a awanni da yawa sama da sauran yankunan duniya, amma duk da haka suna aiki da karancin kayan aiki da kashi 62. / Others
14 Mayu 2025

Suna aiki a sirrance, ba a ganin nasarorinsu a bayyane, da wahala a yaba irin gwagwarmayar da suke yi.

A fadin Afirka, ma’aikatan jinya ne ƙashin bayan kula da lafiya, suna bayar da kulawa a inda babu isassun kayan aiki, an yi wa asibitocin da ake da su yawa, kuma ana yanke shawara kan rayuwa da mutuwa a cikin mummunan yanayi.

Wani sabon rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya yi nuni ga bamancin da ake da shi tsakanin nauyi da kyautatawa - ma’aikatan jinya a Afirka na bai wa marasa lafiya kulawa da kashi 43% a awanni fiye da na sauran yankunan duniya, amma duk da haka suna aiki da ƙasa da 62% na kayan aikin da na sauran duniya suke yi.

A yayin da kusan ma’aikatan jinya miliyan biyu a duniya suka shiga sana’ar tun 2018, Afirka ta kasance mafi ƙaranci. Nahiyar na da kashi 17 na yawan jama’ar duniya, amma tana da kashi 3 na ma’aikatan jinya a duniya.

Sakamakon da ke biyo baya yana da muni

Sudan ta Kudu na da ma’aikatan jinya 3 da ke kula da duk mutum 10,000, ƙasa sosai da matsakaicin abin da ake da shi a duniya. Kashi 76% na ma’aikatan jinya a nahiyar na aiki ba tare da isassun muhimman kayan aiki ba, yayinda ala tilas kashi 58% ka sake amfani da kayan da ya kamata a yi akiki da su sau ɗaya saboda ƙarancin su.

Wannan ba matsalar lambobi ce kawai ba; matsala ce ta neman tsira.

A wani asibitin ƙauyen Kenya, ma’aikaciyar jinya Sanaiyan Torome na fuskantar wannan matsala a kowace rana. A yayin wani aiki da ta yi na tsawon awanni 17, ta taimaka wa wata mai naƙudar ‘yan biyu da cikin ya zo da tangarɗa, ta taimaka wajen haifar wasu jarirai biyu, ta kula da masu zazzaɓin cizon sauro, tare da kwantar da hankalin wani da ya yi hatsari a babur.

Sanaiyan na da wata abokiyar aiki da ke taimaka mata aiki da tsakar dare ba tare da wata matsala ba.

Kula da lafiyar bugun zuciya

Irin waɗannan ne labaran da ba a bayar da su game da ma’aikatan jnya na Afirka da ke aiki cikin rashin kayan aiki wadatattu.

“Ba wai ƙarancin ma’aikata kawai muke fuskanta ba; ba mu da isassun kayan aiki ma.” in ji ma’aikacin jinya Mahamadou Cisse da ke aiki a wani ƙaramin asibiti a Mali, yana ɗauke da wani abin auna hawan jini da ya yage aka ɗinke.

“Ko batun marasa lafiya da ke amfani da gado ɗaya, ko mu da muke sake maimaita amfani da safar hannu, ko zaɓar wane marar lafiya ne zai yi amfani da oxygen - wannan ba shi ne aikin jinya da aka koya min ba,” in ji Mahamadou.

Rahoton Halin da Ma’aikatan Jinya Ke Ciki a Duniya ya bayyana cewa a 2025 a ƙasashe masu arziki kashi 23% na ma’aikatan jinya ‘yan Afirka ne.

“A duk lokacin da wani abokin aiki ya tafi Turai, wani ɓangare nawa na jin cewa nima in tafi,” in ji Chioma Okeke da ke Lagos. “Amma idan na kalli ɗakin yara sai na ce yanzu wa zai kula da waɗannan yaran idan duk muka tafi?”

Ranar Ma’aikatan Jinya ta Duniya, a ake bikinta a duk ranar 12 ga Mayun kowace shekara, ta zama ranar girmamawa ga ma’aikatan lafiya jarumai irin Chioma.

A kauyen Malawi, ma’aikacin jinya James Kalonga na yin tafiyar kilomita 12 kowace rana tsakanin ƙauyuka.

“Asibitina shi ne duk wata bishiya mai bayar da inuwa da muka samu,” ya faɗa, yana buɗe jakarsa ta aiki.

James ya yi wa sama da yara 1,200 allurar riga-kafi a wannan shekarar kawai.

Tsofaffin matsalolin ma’aikatan jinya

Sauyin kula da lafiya da aka samu a Ghana a baya bayan nan, ya haɗa da inganta albashi, da kyautata yanayin aiki, da ɗaukar matakan ƙarin girma, manufar ita ce a rage hijirar ma’aikatan jinya.

Har yanzu, kashi 47% na jama’ar Afirka ba su da isasshen kayan kula da lafiya, ɓangaren aikin jinya na bukatar ƙara masa ƙarfi cikin gaggawa.

Kusan kashi 33 na ma'aikatan jinya a duniya 'yan kasa da shekaru 35 ne, amma a Afirka abin ba haka yake ba.

“Na ga ma’aikatan jinya na yanke jiki suna faɗuwa bayan aiki,” in ji Zuena Mugusha, wata ungozoma a Uganda.

Kashi 42% ne na ƙasashen duniya kawai ke tallafawa ma’aikatan jinya da kula da lafiyar kwakwalwarsu, wanda babban gibi ne, musamman bayan matsalar da annoba ta kawo.

WHO a Afrika ta ƙaddamar da gangami a Ranar Ma’aikatan Jinya ta Ƙasa da Ƙasa da manufofi uku; ɗaukar ninki uku na ma’aikatan jinya a ɓangarorin da babu isassun ma’aikata, da samar da kayan tsaro da kula wa a ɓangarori daban-daban, da samar da tsarin gaggawa don tabbatar da ma’aikatan jinya sun bayar da kulawa ingantacciya.

“Duk da cewa wannan rahoto na ɗauke da labari mai ƙarfafa gwiwar ma’aikatan jinya waɗanda su ne ƙashin bayan kula da lafiya, ba za mu manta da rashin daidaiton da ake samu a duniya a ɓangaren aikin jinya ba,” in ji Darakta Janar na WHO Dr tedros Adhanom Ghebreyesus, kafin ƙaddamar da shirin na bana.

“Ina kira ga ƙasashe da abokan aiki da su yi amfani da wannan rahoto a matsayin alama, da ke nuna mana daga ina muke, a ina muke a yanzu, ina muke bukatar zuwa - nan da nan.”

Ga dubunnan ma’aikatan jinya a Afirka, waɗannan ƙalubale ba wai alƙaluma ba ne kawai; matsaloli ne da ake rayuwa da su.

Wata rana ce a asibitin karkara a Kenya inda Sanaiyan ke aiki. Da sanyin safiya, ta duba injin janareto, tana fatan akwai isasshen mai don ta kunna injin don aikin tiyatar haihuwa da za a yi.

“Ba ma’aikatan jinya kawai muke bukata ba; muna bukatar tsari da zai daraja mu ya kula da lafiyarmu da ta marasa lafiyarmu,” kamar yadda ta faɗa wa TRT Afrika. “Ana yawan kiran mu da jarumai. Amma jarumai ma na ƙukatar tallafi.”

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us