A yayin da kyamar Musulunci ke yaduwa a nahiyoyi, kwararru na gargadin cewa nuna kyamar Musulunci, alamun nuna wariya a yau, ba wai matsala ce ta Musulmai kawai ba, lamarin ya zama rikicin da ke barazana ga tushen dimokuradiyya, hakkokin dan adam da zamantakewa.
Kwararrun kasa da kasa a ranar Lahadi sun yi babban kira ga duniya da ta dauki matakan gaggawa kan ta’adar da suka ce tana kara yaduwa cikin sauri - a rana ta karshe ta taron a yayin wani zama mai taken ‘Fuskantar Nuna Bambanci da Wariyar Launin Fata a Karni na 21’ da ya gudana a birnin Antalya na hutawa da ke gabar Tekun Bahar Rum a Turkiyya.
“A yayin da ake kara yawan neman hade al’umma waje guda, sai a ga nuna wariya na kara bayyana kansa sosai,” in ji Evren Dagdelen Akgun, Wakiliyar Musamman kan Yaki da Nuna Kyama da Hantarar Musulmai, ta Kungiyar Tsaro da Hadin Kai a Turai (OSCE).
Da yake kawo alkaluma Hukumar Kare Hakkokin Dan’adam ta Tarayyar Turai, ta yi karin haske cewa daya daga cikin Musulmai biyu a Turai na fuskantar nuna wariya, idan ma ba a samu hantara ba kenan, a kowace rana.
"Magance alamun cutar ba zia mayar da mu zama al’umma dunkulalliya ba,” ta yi gargadi. “Nuna Kyama ga Musulmai gaskiya ne, kuma ko ma da wanne irin suna za a kira shi, wani nau’i ne na nuna wariya.”
Akgun ta yi nuni ga mummunan yanayin da nuna wariya da kyamar Musulunci suka shiga cibiyoyin dimokuradiyya, suka lalata wakilci, ‘yanci da adalci. Wannan gurbataccen abu na lalata halascin dimokuradiyyar kanta, kuma na sanya da wahala a kalubalanci wadannan halaye.
‘Ba matsalar Musulmai kadai ba ce, batu ne na hakkokin dan adam’
Ambasada Mehmet Pacaci, Wakilin Musamman na Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya kan Yaki da Kyamar Musulunci, a Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC), ya fitar da yadda duniya ke kallon lamarin.
“Duk da babban kokarin da aka yi ta hanyar gwagwarmayar kare hakkokin dan adam da gyare-gyaren dokoki, nuna wariya da bambanci na ci gaba da bayyana da habaka,” in ji shi. Ya bayyana nuna wariya na zamani a matsayin “zaunanne a cikin siyasa, tattalin arziki da zamantakewa.”
Pacaci ya kawo alkaluma masu rikitarwa: a Amurka, kusan korafin mutane 9,000 aka samu na an nuna musu wariya a 2024 - mafi yawa tun 1996.
A Turai, Ganin nuna kyama ga Musulunci ya karu da kashi 43, inda a Australia da Gabas Mai Nisa, hantara ta ninka a shekaru biyun da suka gabata, inda ya fi kuma shafar mata manya da yara.
Wadannan alkaluma ba kididdiga ba ce kawai,” in ji Pacaci. “Suna wakiltar mutane na gaske, iyaye mata, iyaye maza da yara da ke rayuwa a cikin tsoro saboda addininsu.”
Ya soki manyan kafafen yada labarai saboda kara ta’azzara Nuna Kyamar Musulunci da ra’in tuggu, inda suka shiga tattuanawar al’umma da samar da tsare-tsare da manufofin cigaba.
“Yadda aka mayar da wannan tsana kamar ba komai na da mummunan sakamako,” ya yi gargadi.
“Na lalata zaman tare, manufofin dimokuradiyya da zamantakewa…. Nuna wariya ga Musulmai ba matsalar Musulmai kadai ba ce, batu ne na hakkokin dan adam.”
Nuna wariya ya zama gama-gari a Turai
Marion Lalisse, jami’ar Tarayyar Turai kan yaki da Kyamar Musulmai a Hukumar Tarayyar Turai, na da wannan ra’ayi.
“Dimokuradiyya, muhimman hakkoki, doka da oda - ana yawan amfani da su ta mummunar hanya,” in ji ta. “Bin dimokuradiyya ba ya nufin za ka samu sakamako mai kyau ba ne. Na nufin kana yin nasara a kowace rana.”
Ta jaddada cewa nuna wariya a Turai ya zama gama-gari, ba Musulmai kadai ake nuna waba, har ma da bakaken fata, Rumawa, ‘yan Asiya da Yahudawa.
“Romawa ne kusan mutanen da aka fi nuna wa tsana a cikin al’ummunmu,” ta fada, tana mai lura da cewa hakan na faruwa duk da gwagwarmayarsu.
Lalisse ta bayyana muhimmancin fito da nuna wariyar da aka tsara, ba wai nuna wariya tsakanin mutane biyu ba.
“Nuna wariya ya fito ne daga duba ga kabilanci zuwa ga al’adu da addinin mutum,” in jita, tana mai bayyana damuwa ga Musulmai a fadin duniya, ciki har da a kasashen India, China, Myanmar, Amurka, Canada, Australia da Turai.
ta kuma kawo batun kalubalen da Hukumar Tarayyar Turai ke fuskanta wajen daidaita manufofin nuna wariya da ‘yancin mulkin kasa.
A yayin kasashe mambo suka rike muhimman matsayi, ta jaddada cewa rawar da Tarayyar Turai za ta taka ita ce goyon baya - ba wai nuna iko ba - ga kokarinsu.
Ta kuma tabo batu karuwar nuna tsana a siyasa da kafafen yada labarai. Babbar damuwar ita ce, yadda kafafen yada labarai ke taka rawa wajen kakamai masu cutarwa game da Musulmai.
“A bayyane take karara, akwai kafafen yada labarai da ke aiki tukuru wajen ajje maganganu na gaskiya, musamman nuna tsana da wariya ga Musulmai, amma akwai wasu da ke wasa saboda sun san za ka iya samun kudi da yin hakan, kuma za ka iya bayar da rahotannin Musulmai ta mahangar ta’addanci da gudun hijira, wanda… ke janyi rikici tsakanin al’umma,” ta yi karin haske.
Domin yaki da hakan, Tarayyar Turai na aiki tare da ‘yan jaridu, hukumomin dabbaka dokoki, da majalisun ‘yan jaridu don wayar da kan jama’a.
Lalisse ta yi karin haske kan hadin kan da Tarayyar Turai ke taimakawa kamar Kawancen Turai na Garuruwa don Yakar Nuna Wariya, wanda ya hada da Istanbul da Antalya, a matsayin wuraren da suka zama tushen sauyi.
Kasashe Masu ‘Yanci da Dimokuradiyya ma ba su tsira ba
Salman Sayyid, farfesa a Jami’ar Leeds kuma mai yawan yin magana kan launin fata da rayuwa bayan mulkin mallaka, inda ya kawo batutuwa na falsafa.
“Nuna Kyama ga Musulunci ba matsalar Yammacin duniya ba ce. Matsala ce ta duniya baki daya,” in ji shi.
Ya bayyana cewa a yayin da ake bayyana dimokuradiyya da ‘yanci a matsayin abin murna da tubalan cigaba, amma kuma sun zama “na da dacewa da nuna wariya,”.
Sayyid ya yi karin haske kan wasu tubalan nuna wariya a zamanin yau: “Babu wanda zai so a kira shi da mai nuna wariya, amma ba su damu da aikata nuna wariyar ba,” yana nuna yadda manyan ‘yan siyasa ke yawan yin manyan bayanai game da tafiya tare da kowa amma kuma suke bayar damar nuna bambanci.
Ya jaddada cewa Nuna Kyamar Musulunci ba wai nunakyamar al’adu ba ne kawai ko son kan daidaikun mutane, har ma da “sakamakon siyasa daga tsarin siyasa,” da ake amfani da su a matsayin yarjejeniyar zamantakewa tsakanin shugabanni da wadanda ake shugabanta.
Nuna kyama ga Musulunci hanya ce da ake sake rubuta yarjejeniya tsakanin shugabanni da wadanda ake shugabanta,” in ji shi, yana mai karawa da cewa a yanzu ta zama binda aka amince da shi a zamantakewa.
Sayyid ya kuma yi gargadin cewa Nuna Kyama ga Musulunci ba Musulmai kawai yake shafa - tasirinta ya kai da nisa, kamar yadda aka gani a manufofi irin na Trump na hana tafiya da tun farko ya fara saka wa Musulmai, amma a karshe ya shafi wasu al’ummun kamar “masanin kimiyyar Faransa da ba Musulmi ba ne.”
A karshe, ya karkare da cewa yaki da Nuna Kyamar Musulunci ba yaki da ‘yan tsiraru marasa rinjaye ba ne kawai “har ma da yaki don tabbatar da adalci a tsakanin jama.”
‘Matsala da ke damun Turai da ma duniya…’
Sener Akturk, farfesa a siyasar kamantawa a Jami’ar Koc, ya bayar da karin haske mai muhimmanci zuwa ga tushen tsararriyar nuna wariya da kuma alakarta da kamantarwa ta rashin daidaito.
Ya fara da yin warwara kan sananniyar akida: “Matsala da ke bibiyar Turai da duniya - wannan ita ce matsalar daidaito da siffanta mutane da adalci.”
Akturk na muhawarar cewa mafi yawan Nuna Kyama ga Musulunci a yau ya bullo ne daga tirjiya zuwa ga bukatar asalin daidaito - bukatar da har yanzu a Turai da Arewacin Amurka aka kasa cim-mawa.
Ya lura da cewa yawan jama’ar Musulmai ba sa samun a isar da sakonninsu a siyasa yadda ya kamata.
A kasashen Turai 26, Musulmai na rike da kashi daya cikin uku na kujerun majalisun dokoki idan aka akwatanta da yawan su.
A Faransa, duk da kasar ta fi kowacce kasar Turai yawan Musulmai, majalisar dokokin kasar na da mambobi Musulmai ‘yan kadan - kasa da 40 da ya kamata a ce suna da su don daidaita wakilci.
Sama da alkaluma, Akturk ya fito karara da matsalar ‘wakilci’ - Musulmai da dama da aka zaba ba sa wakiltar damuwar al’ummunsu.
Ya kuma kalubalanci bambancin da ake kawo wa na ‘Yan gari da zuwo” don nuna wariya ga Musulmai wanda mafi yawancinsu na rayuwa a Turai tsawon zamaninnika, yana kawo misali da Musulman Spaniya, Portugal da Sicily, yana cewa bayyana Turai a matsayin “nahiyar Kiristanci” na kawar da arzikinta da tarihinta na mai addinai da dama.
Akturk ya karkare da kira da a sauya salon yadda ake tattauna al’ummu. Ya ce babban batun shi ne dole ne a tabbatar da “dukkan mutane, ba tare da duba ga addini ko asali ba, su zauna waje guda kuma a mu’amalance su da daidaito da girmamawa sannan su samu dama iri guda wajen siffanta su a kafafen yada labarai.”
‘Dole ne al’adu daban-daban su zauna waje guda’
Mafi yawan wadanda aka tattauna da su sun yarda cewa wanzuwar al’adu da dama a lokaci guda ba sararin zama tare kawai ke kawo wa ba, har ma da kasnacewa babban jigo na yaki da Kyamar Musulunci, nuna wariya da bambanci.
Kamar yadda Sayyid ya bayyana, a yau kusan za a ce an arsa komai gamd a wanzuwa al’adu da dama waje guda kuma su zauna lafiya.
“Muna bukatar sake duba me ya sa yake da muhimmanci a wajen mu zama masu aminta da al’adun da ba namu su kasancewa tare da mu,” in ji shi, yana mai cewar zaa da sauran al’adu wajibi ne ba wa zabi ba ne.
A nasa kaulin, “Bakunta na zuwa ta hadu da wanda ba ta sani ba, kuma muna kara samun hikima ne a lokacin da muka zama al’ummu mabambanta da ke zama tare.
Akgun na OSCE na kuma bayyana cewa: “'Kalmomin wanzuwar al’adu’ ya ksance tare da mu tsawon lokaci…. kuma z ata dauwama.”
Wadannan ra’ayoyi na karfafa cewar rungumar al’adu mabambanta ba salon zamantakewa ba ne kaiwa mai kyau, har ma da batun al’adu na dole wajen samar da al’ummu masu adalci da tsaro.
Tattaunawar da aka yi a Antalya ta bayar da mafita: amincewa da nuna kyama ga Musulunci a matsayin nuna wariya; dora alhakin kalaman nuna tsana kan kafafen yada labarai da ‘yan siyasa; taimaka wa ayyyuka daga tushe da aka samar don gina al’umma mai mutane mabambanta, da kuma amfani da wanzuwar al’adu da dama a matsayin mafita ba wai barazana.
A yayin da Pacaci ke takaita wa “Wannan kalubale ne da ke barazana ga daraja da tsaron wadanda ake nuna wa wariya. Dole mudaki mataki, ba ga Musulmai kawai ba - ga dukkan ‘yan adam.”