Tasirin ayyana harshen Hausa a matsayin harshen ƙasa a Nijar
AFIRKA
4 minti karatu
Tasirin ayyana harshen Hausa a matsayin harshen ƙasa a NijarNijar ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta shelanta harshen Hausa a matsayin Harshen Ƙasa. Batun zai ba da gagarumin cigaba ga Hausa wanda a Afirka shi ne harshen asali mafi rinjayen masu amfani da shi.
/ AP
9 Afrilu 2025

A ranar 31 ga Maris din 2025 ne gwamnatin ƙasar Nijar ƙarƙashin Shugaban mulkin soji, Janar Abdourahmane Tiani ta amince da harshen Hausa ya zama Harshen Kasa a duk faɗin ƙasar mai al’umma kusan miliyan 30.

Hausa ya maye gurbin harshen Faransanci wanda a baya shi ne harshe ɗaya tilo da gwamnati ta amince da matsayinsa a duk kasar.

A yayin babban taron tattaunawa kan makomar Nijar da aka yi a watan Fabrairun shekarar nan a birnin Niamey, an amince da ƙudurori daban-daban ciki har da duba harsunan da ake magana da su a ƙasar kamar su Hausa da Zabarmanci da Fulatanci da Kanuri da kuma Larabci.

Daga nan ne aka zaɓi harshen Hausa a hukumance ya zama Harshen Ƙasa, sannan aka ƙara harshen Ingilishi tare da harshen Faransanci a matsayin harsunan aiki.

Wannan mataki ne da ke nuna kishin ƙasa, da kishin asali, da ma kishin harshe da gadon al’ummar kasar.

Me ya sa aka zaɓo Hausa?

A Nijar dai, ƙididdiga ta tabbatar da cewa kaso 80 cikin 100 na al’ummar ƙasar suna amfani da harshen Hausa. Sannan duk da zaman Faransanci harshen hukuma, ƙasa da kashi 20 na al’ummar Nijar ke aiki da shi.

A makonnin baya, Nijar da Mali da Burkina Faso sun shelanta ficewa daga ƙungiyar ƙasashe masu amfani da harshen Faransanci, wato Organisation Internationale de la Francophonie (OIF).

A cewar Dr. Alamuna Nuhu, malami a shashen nazarin harsuna a Jami’ar Jihar Kaduna da ke Nijeriya, “Harshen Hausa ya fara ƙwato matsayinsa na daɗaɗɗen tarihi wajen haɗa kan al’ummar ƙasar Nijar”.

Da ma can harshen Hausa ya kasance abin alfaharin al’ummar yankin tsohuwar ƙasar Hausa, wadda ta zamo wani babban ɓangare na ƙasar Nijar a zamanin yau.

Harshen Hausa ya kasance harshen kasuwanci tun tale-tale, tsakanin mazauna da fatake a yankin Afirka ta Yamma, da ta Tsakiya, da ma ta Arewaci, inda ake amfani da Hausa a sama da ƙasashe 10, daga Nijar, Ghana, Nijeriya, Kamaru, Chadi, Sudan, da ma Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya.

A duniyar yau, an ƙiyasta cewa mutum tsakanin miliyan 100 zuwa 150 ne suke magana da harshen Hausa.

Tabbatuwar fata

Shi ma wani masani a Nijeriya, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya yaba wa gwamnati da al’ummar ƙasar Nijar, bisa wannan ƙoƙari na karrama harshen gida zuwa matsayin harshen ƙasa.

A cewar Farfesa Adamu, “Wannan ya darajanta Hausa kamar yadda ƙasashen Gabas na Afirka, wato Tanzania da Kenya da Uganda, da sauransu suka ɗaukaka harshen Swahili”.

Ya ƙara da cewa wannan cigaba ya zamo cikar burin Marigayi Farfesa Muhammad Hambali Jinju, shahararren manazarcin harshen Hausa ɗan asalin garin Jinju da ke ƙasar Nijar, wanda ya koyar a jami’o’i daban-daban a duniya, kuma ya tsaya kai-da-fata don ganin an koyar da harshen Hausa da Hausa, maimakon da Ingilishi.

Tun a shekarar 1990, Farfesa Hambali Jinju ya yi kira kan a ɗaukaka martabar harshen Hausa, inda ya rubuta cewa, “Wajibi ne Jamhuriyar Nijar da Tarayyar Nijeriya su himmatu da gaske wajen ɗaga matsayin Hausa zuwa matsayin harshen ƙasa kuma na mulki da koyarwa.”

Bambanci tsakanin harshen ƙasa da harshen hukuma

A cewar Dr. Alamuna Nuhu, harshen ƙasa shi ne harshen da ke da alaƙar gargajiya da al’ummar ƙasa, saboda kasancewarsa mafi rinjaye da kuma alaƙarsa da tarihin mutanen ƙasar.

Shi kuma harshen hukuma, shi ne harshen aiki a hukumance, ko da kuwa ba shi da asali a ƙasa, kamar dai yadda ake gani a yawancin ƙasashen da aka yi wa mulkin mallaka a tarihi, waɗanda aka tilasta musu amfani da harsuna kamar Ingilishi da Faransanci.

Duka masanan na ganin ɗaga darajar harshen Hausa a Nijar zai taimaka wa al’ummar harshen a fannin karatu da kishin-kai da rage mummunan tasirin mulkin mallaka a tunanin al’ummar Afirka.

A yanzu dai za a iya cewa ana kyautata fatan nan gaba harshen Hausa ya samu ƙarin daraja zuwa harshen aiki da kuma koyarwa a Nijar, wataƙila har ma a wasu ƙasashen masu amfani da Hausa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us