A lokacin da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan ya ce “ba ma kallon manufar kasashen waje a matsayin mai takaita ga iyakokin yankuna kawai,” yana bayanin da ya haura manufofin diflomasiyya a wajen Taron Diflomasiyya na Antalya karo na 4 na 2025.
Fidan na bayyana irin dabarun da ya kamata a bi wajen sake fasalin yadda ake tafiyar da duniya. A manufar, ya bayyana diflomasiyya, ba wai rabuwar kai ba, a matsayin dabarar mu’amala da aka fi amfani da ita a duniya.
Ya yi kira ga “dawo da adalci ta hanyar diflomasiyya” wanda ke bayyana taken Taron: Dabbaka Diflomasiyya a Duniyar da Kawuna SUka Rarrabu.
Na kuma fito da aniyar Turkiyya ta zama mai shiga tsakani ta gaskiya a yankuna masu yawa da ke fama da rikici.
Domin kalubalantar kara rincabewar rikicin Gaza zuuwa Ukraine, kuma a yayin da ake rikici tsakanin kasashen duniya, Taron ya sanya diflomasiyya zama hanya daya tilo da za ta samar da zaman lafiya a duniya.
An sadaukar da ranar farko ta bude taron ga Gaza, wani zabi da ke bayyana fifikon da Turkiyya ta baiwa adalci a darajar dan adam.
Enrique Jaime Calderon, jakadan El Salvador a Ankara ya fada wa mai wannan rubutu: “A wannan dab’in, an yi karin haske da bayanai game da muhimmancin hadin kan kasashe don cim ma manufa guda da diflomasiyya a tsarin tafiyar da duniya a yau.
Na yi amanna kan karfin tattaunawa, sulhu da bukatar taruka irin su ADF wajen warware kalubalen duniya.”
Ya kara da fadin: “Ba ni da tantama cewa Taron Diflomasiyya na Antalya zai tattara alfanun tarukan da aka yi tsawon shekaru tsakanin kasashe da niyyar cim ma manufa guda don magance manyan batutuwa da suka shafi duniyarmu.”
Taron ya samu halartar sama da mutane 6,000 daga kasashen duniya 155, ciki har da shugabannin kasashe 21 da gwamnatoci, da ministoci 64.
Al Sharaa da diflomasiyya a aikace
Daga cikin abubuwan diflomasiyya masu muhimmanci a wajen taron shi ne halartar Ahmed Al Sharaa, shugaban gwamnatin rikon kwarya ta Syria. Halartarsa ta sake fito da Sham zuwa ga fagen hadin kan kasashen duniya.
“Halartarmu na zuwa ne saboda yadda Tarayyar Larabawa ta Siriya ta amince cewa tattaunawa da dislomasiyya ne mafi muhimmancin hanyoyi wajen warware rikici da samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankinmu da ma duniya,” in ji Al Sharaa.
Al Sharaa ya yi amfani da taron don ganawa da manyan mutane, ciki har da Ilham Aliyev n Azarbaijan, Firaminista kuma Ministah Harkokin Wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan, da Shugaban Kasar Kosovo Vjosa Osmani.
Wadannan taruka na bayyana niyyar Syria da yadda take son ta ake shiga fagen diflomasiyyar kasa da kasa tare da shiga ayyukan samar da zaman lafiya a duniya a Gabas ta Tsakiya da ma wajen yankin.
Wadannan kalamai a bangaren Syria na kuma bayyana smaun sauyi zuwa ga tafiya tare da kowa, sake gina kasa, da mallakin yanki duba ga ayyukan samar da zaman lafiya.

Tattauna game da Syria a Taron Antalya. ta mayar da hankali ga tafiya da kowa, sake gina kasa da mallakin yankin ta sigar samar da zaman lafiya. Photo: AA
Sakon Rasha kan “hadin kai da zama lumana”
Shiga tsakanin ministan harkokin wajen Rasha, Sergey Lavrov, wanda ya yi amfani da taron don sake bayyana matsayin Rasha kan yaki a Ukraine da ma tsarin tafiyar da duniya.
Lavrov ya ce “A yanzu babu batun hadewar duniya waje guda kan tattalin arziki,” yana dora laifi ba a kan Donald Trump ba, sai a kan Joe Bidem saboda “Rusa” tsarin sha’anin kudi na duniya ta hanyar saka takunkumai.
“Ba Trump ne ya rusa ba, Biden ne a lokacin da ya kawo takunkumai tare da mayar da su makaminsa na cim ma manufofin kasashen waje.”
Da yake bayani a rana ta biyu ta taron na kasa da kasa, Lavrov ya ce Trump “ya fahimci lamarin sosai, sosai, sosai game da abinda ke faruwa (a Ukraine) sama da duk wani shugaba na Turai,” yana mai bayyana yadda shugaban Amurkan ya fahimci rikicin Rasha da Ukraine, ba kamar takwarorinsa na Turai ba.
An ajje kalaman na hanzari na Lavrov ga Kudancin Duniya. “Sabon tsarin tafiyar da duniya zai yi aiki ne idan wadannan yankuna suka farfado,” in ji shi, yana mai bayar da misali ga Afirka, Asiya, Latin Amurka, da Gabas ta Tsakiya.
Kamalansa sun zama ababan dubawa wajen zuzzurfan hadin kai da manyan kasashen duniya irin su China da India, da ma kungiyoyi irin su Kungiyar Hadin Kan Shanghai, ASEAN da Kungiyar Tattalin Arziki ta Eurasia da ma wasun su.
“Kuma kimanin shekaru 10 da suka shude, mun fara gina wadannan gadoji ba tare da samun wani abu a zuciya ba game da tsaro, amma sai a bangaren tattalin arzikim jigilar kayayyaki, ana neman hanyoyin hadin kai da hada hannu waje guda. Wannan alkari ne aka yi. Muna kiran sa da Babban Hadin Kan Eurasia,” in ji shi.
Burin Latin Amurka: Kasuwanci, karfin iko da tafiya da kowa
Taron ya bayar da dama ga shugabanni, jami’ai da kwararru daga Latin Amurka da Caribbean su yi musayar ra’ayoyi d abatutuwa don magance wannan gaba, daga kalubalen siyasa, zamantakewa da dmaarmakin tattalin arziki a duniya mai sauyawa.
A daya daga cikin zaman da aka yi, mai taken “Kawancen Duniya Duba ga Yakin LAC,” Noemi Espinoza Madrid, ta Kungiyar Kasashen Caribbean (ACS), ta yi jawabi mai gamsarwa.
Ta tabo yanayin da yankin ke ciki, tana kiran Caribbean da '“yankin zaman lafiya” da ke da dimbin arzikin kasa da al’adu, wadanda aka tsara su don bayar da gudunmawa a lokutan rikici a duniya.
Ta ce Caribbean ya mallaki albarkatun kasa da dimbin al’adun da ya ci a ce tana taka babbar rawa wajen warware rikicin duniya.
Julio Eduardo Orozco Perez, Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Guatemala, ya bayyana muhimmancin kanana da matsakaitan sana’o’i wajen cigaban yanki.
“Shigar da bangare mai zaman kansa na taka muhimmiyar rawa ga cigaban yanki. Dole ne mu habaka kanana da matsakaitan sana’o’i, don ba su dama su habaka tare da samar da ayyukan yi, wanda ke kuma taimaka wajen kula da gudun hijira,” in shi.
Hector Cardenas, Shugaban Majalisar Alakar Kasashen Waje na Mexico (COMEXI), ya yi nuni ga tari mai harshen damo: “Dabarun Mexico na tattare kan kare wa da karfafa alakarmu ta 'Mexico-Amurka0Kanada (T-MEC), inda a lokaci guda ake neman sabbin damarmaki.
Yana da muhimmanci mu shigar da kawaye irin su Turkiyya don fadada kasuwanci da damarmakin zuba jari.”
Carlos Guevara Mann, Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Panama, ya yi kiran fadada alaka: “Dole ne kasashen Latin Amurka su bunkasa kasuwancin yanki ta hanyar kungiyoyi irin su ACS, Mercosur da yarjejeniyar yankin Tsakiyar Amurka.” in ji shi.
“Ya zama dole mu nemi sabbin kawaye irin su Turkiyya don fadadawa d akarfafa alakar tattalin arzikinmu.”
Zaman na hadin kan tattalin arzikin duniya ba tattaunawa kawai ba ce: sake tabbatar da habakar dabarun girmamar yankin ne da kuma shirin sa na neman a samu tsarin tafiyar da duniya mai adalci.
A yayin da ake ci gaba da tattaunawa kuma hadin kai ke kara yaduwa, a duniyar da ake da rarrabuwar kai, gida gadoji na da matukar muhimmanci kuma abu ne da ya zama wajibi.