Illar da fasa-ƙwaurin kuɗaɗe a iyakokin Nijeriya ke yi wa tattalin arzikin ƙasar
NIJERIYA
5 minti karatu
Illar da fasa-ƙwaurin kuɗaɗe a iyakokin Nijeriya ke yi wa tattalin arzikin ƙasarKasancewar Nijeriya ce ta fi girman tattalin arziƙi a Afirka, ƙasar na fama da matsalar masu aikata laifukan da suka shafi hada-hadar kuɗaɗe, da kuma safarar tsabar kuɗi a iyakokin shige da fice.
/ Reuters
27 Maris 2025

Hukumar yaƙi da almundahana a harkokin hada-hadar kuɗi ta Nijeriya, tana mayar da hankali kan nau’o’in laifuka da suka haɗa da halatta kuɗin haram, da bugawa da safarar kuɗin jabu, da ma wasu salo-salo na zamba da kuɗaɗe.

A kwanan nan, Hukumar Yaƙi da Masu Ta’annati ga Tattalin Arziƙi, wato EFCC ta gabatar da wani fasinjan jirgin sama da ake zargi da laifuka. An kama shi ne a watan Maris a filin jirgi mafi girma a ƙasar da ke jihar Legas, inda cibiyar tattalin arziƙin ƙasar take.

A cewar bayanan shigar da ƙara na EFCC, wanda aka kama ɗin ya gaza ayyana tsabar kuɗi dala $578,000 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a Lagos. Ana zarginsa da laifuka huɗu “da suka haɗa da halatta kuɗin haram da zambar jabun kuɗi”.

“Ana samun tarin fasinjojin ƙasashen waje da ake kamawa da kuɗaɗen da suka ƙi bayyanawa yayin bari ko shigowa cikin Nijeriya. Amma lamarin ya fi ƙamari a shekarun baya”, cewar Shuaibu Idris Miqati, wani masanin tattalin arziƙi a Nijeriya.

Mr Miqati wanda shi ne shugaban wata cibiyar nazarin hada-hadar kuɗi a Legas mai suna Time Line Consult Limited, ya ce, “Waɗannan alamu ne na ƙamarin ayyukan almundahana da laifukan da suke faruwa a ciki da wajen ƙasa.

“Mutane na amfani da kuɗaɗen manyan ƙasashen waje saboda sun fi sauƙin ɗauka sakamakon fifikon darajarsu sama da kuɗin Nijeriya, Naira. Haka kuma mutane na tsoron ɗaukar kasada yayin tafiya da maƙudan kuɗi da suka samu daga ayyukan laifi ta hanyoyin da hukuma ta san da su”.

Tafiya da haramtattun kuɗaɗe

Safarar tsabar kuɗi daga waje zuwa Nijeriya ko da na riba ne, ko na ayyukan laifi a ƙasashen waje, yana da wahala saboda dokokin hukumar shige da fice da suka haramta ɗaukar tsabar kuɗi sama da dalar Amurka dubu goma.

Ana samun rahotannin kama mutane a filayen jiragen sama, da matafiya ƙasashen waje masu safarar kuɗi daga haramtattun kasuwanci, ciki har da fataucin mata, da fataucin yara, da fataucin ƙwayoyi, da haƙar haramtattun ma’adanai, da munanan hanyoyin samun-kuɗi.

Halatta kuɗin haram ya ƙunshi laifukan safarar kuɗi tsakanin wurare ko iyakoki, ko wani tsarin ɓoye tushen kuɗaɗen da aka samu ta haramtattun hanyoyi. Yakan iya ɗaukar salon shigar da kuɗaɗen haram ta bankuna ko sahihin kasuwanci.

A cewar Shuaibu Miqati, “Hada-hada a ba a cikin tsarin bankuna ba tana lahanta arziƙin ƙasa. Idan babban kaso na hada-hadar kuɗi ta zama a ƙarƙashin-ƙasa kuma ba a lura da shi ba, alƙaluman tattalin arziƙi kamar GDP sukan zama ba daidaitattu ba, wanda ke tasiri kan tsarin haraji, da tsimi, da na tattalin arziƙi.”

Baya ga iza wutar tsarin zaluncin tsiraru, da halatta kuɗin haram, kuma yakan haifar da munanan laifuka kamar fataucin ƙwaya, da laifukan intanet, da ƙin biyan haraji, da safarar mutane, da ta’addanci, da rikicin siyasa, da ɗaukar nauyin munanan laifuka kan ƙasashe ko al’umma.

Gujewa hauhawar farashi

Me yaka sa mutane su fara hada-hada da kuɗaɗen ƙasashen waje, da kuma ɗaukar kasadar fasa-ƙwaurin kuɗaɗen ta filin jirgin sama, duk da sun san da gagaruman matakan tsaro da saka-ido a irin waɗannan wurare?

Miqati ya yi nuni da hauhawar farashin da ake fama da ita a Nijeriya, wadda ke lahanta arziƙin magidanda da masana’antu.

Ya ce wannan ne sanadin ƙaruwar sha’awar da mutane ke yi ta “zuba jari” a kuɗaɗen waje, waɗanda ake ganin sun fi tabbas wajen gujewa karyewar darajar kuɗi.

Akwai masu yi wa mutane dakon kuɗi da ke ɗaukar tsabar kuɗi da aka samo ta haramtacciyar hanya, su shigar da su ta iyakoki. Suna amfani da hanyoyi na zahiri da munana, ciki har da yi wa jami’an tsaro dabara.

A ɗaya cikin laifukan da EFCC ta bincika, an kama wanda ake zargi a Legas da ya zo daga Johannesburg a jirgin kamfanin South African Airways ranar 19 ga Maris, 2025.

A wajen ayyana kuɗin da ke tare da shi, ya faɗi rabin jimillar kuɗi dala $578,000, sannan ya ɓoye saura a “wasu fakitai”.

Ƙaruwar saka-ido

A wani abu da Miqati ya kira babban cigaba a harkar tsaron iyaka, da lura da fasinjoji, da saka-ido a harkar hada-hada a Nijeriya, cikin watan Maris, an sake kama wani fasinja da dala $1.154 da kuma riyal ɗin Saudiyya 135,900.

Lamarin ya faru a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, wanda shi ne mafi yawan aiki a arewacin Nijeriya wanda ke jihar Kano, wanda shi ne birnin kasuwanci na biyu a ƙasar.

An kama kuɗaɗen da fasinja ya ƙi bayyanawa yayin tafiya, ɓoye a cikin wasu fakiti da aka shigo da sunan fakitin dabino, a wajen wani fasinja da ya iso daga jirgin Saudi Airline daga Saudiyya.

Bayan kamen, an tura shi wajen EFCC don bincike da ɗaukar matakin shari’a. Dokokin Nijeriya kan hada-hadar kuɗi sun tanadi hukuncin karɓe kuɗaɗen da aka ɓoye, da mallaka su ga gwamnatin Tarayyar Nijeriya.

Masana kamar Miqati, sun yi imanin cewa tsarin hada-hadar kuɗi a Nijeriya yana fuskantar gagarumin ƙalubale.

Babban bankin ƙasar yana yaƙi don magance fasa-ƙwaurin kuɗi, da kuma haɓaka shiga harkar bankuna a wajen ‘yan ƙasa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us