Da farkon ganin su za ku ga babu wani abu sabo tattare da katafilolin da ke jujjuya kasa a wuraren gini a tsakiyar Isra’ila, amma idan ta matso kusa-kusa, za ku gani karara cewa ai ba su da ma matuki, dakin zaman direba babu kowa a ciki.
Wannan wani nau’i ne na katafilar da aka samar da fasahar zamani ta kere-kere wadda ae iya sarrafa ta daga nesa, kuma a wannan karon ana sarrafa su ne daga wani sansanin baje-kolin kayan soji da ke Alabama.
Injiniyoyi sojoji da kwararru na cewa motocin da aka ba wa sunan ‘Robdozer’ - samfurin katafila buldoza marar matuki kirar D9 - ta kasance makomar motocin yaki da ake sarrafa su daga nesa.
Tsawon shekaru sojojin Isra’ila na amfani da katafila samfurin D9 a filin daga wajen rufe hanyoyi ko bude su ga dakarun da ke matsowa, kwashe buraguzan gini da baje hanya.
Amma tun bayan fara yakin Isra’ila a Gaza a watan Oktoba 2023, sannan daga baya a Lebanon, sojojin Isra’ila sun dinga amfani da motar marar matuki a kokarin habaka ayyukanta a fagen daga, da rage hatsarin da dakarunta ke fuskanta.
“Manufar ita ce ya zama babu mutum a wajen matukin katafilar,” in ji Rani, wanda tawagarsa ce ta samar da motocin marasa matuka a Masnaa’antar Kera Jiragen Sama ta Isra’ila.
A lokacin yakin Gaza, sojoji sun fi amfani da motocin marasa matuka, wadda na iya yin aiki sosai sama da a ce mutum ne ke sarrafa ta”, in Rani, ya yi amfani da sunansa na farko kawai sabod adalilai na tsaro.
A yayin da irin wadannan motoci da wasun su ke aiki tare da mutane, wadnda za a samar a nan gaba za su zama masu sarrafa kansu, wanda ke bayyana damuwar doka da ka’idoji kan makomar yaki a nan gaba da ba a samar da wasu dokoki a kan ta ba, wadda kuma yakin Isra’ila a Gaza ke sake ma lamarin salo.
'Sauyin salo a filin daga'
Ci gaba da amfani da manyan kayan yaki na zamani da Isra’ila ke yi a fagen daga, daga garkuwar makamai daga sama zuwa ga kayan fasaha masu aiki da Kirkirarriyar Basira, batu ne da aka san da shi amma kuma ana sukar sa saboda rashin daidai, rashin saka dan adam a gaba da yiwuwar karya dokokin kasa da kasa.
Masu nazari na cewa yadda Isra’ila ke ci gaba da kai Robdozer zuwa Gaza na bayyana dabi’’ar da ake gani yau a duniya ta koma wa amfani da manyan kayan yaki masu sarrafa kansu, irin su motocin daukar sojoji da ae sarrafa su daga nesa kuma suke aiki kamar Drone.
Wani jami’in sojan Isra’ila, wanda ya nemi da a boye sunansa sbaoda karfin maganar, ya fada wa AFP cewa sojojin na amfani da “kayan yaki masu sarrafa kansu sama da shekaru goma da suka wuce, amma da kadan-kadan, a yanzu kuma ana amfani da su sosai”.
Dakaru a yanzu na iya sarrafa kayan yaki ba tare da shiga ‘iyakar makiya’ ba.
Andrew Fox, tsohon jami’in soj Birtaniya mai ritaya kuma babban mai bincike a Kungiyar Henry Jackson da ke Landan, ya ce kamar sojojin Isra’ila ne na farko da suka fara amfani da manyan motocin yaki da ake sarrafa su daga nesa a filin daga.
“Babban cigaba ne” wato “Salo ya canja” a filin daga, ana yin ayyuka daga nesa kuma mafiya kyau da karanci hatsari ga ma’aikata.
“Wannan ce makoma,” in ji John Spencer, shugaban sashen nazarin yaki a Cibiyar Koyon Yaki na Zamani ta Amurka da ke West Point.
Da yawa na ta kokarin gwaji, amma ba wand aya kai su filin daga kai tsaye a yakin zamanin nan,” ya kara fada. “Ta musamman ce sosai”.