Mata a Afirka sun samar da dabarun tsira daga ƙalubalen sauyin yanayi
AFIRKA
6 minti karatu
Mata a Afirka sun samar da dabarun tsira daga ƙalubalen sauyin yanayiMatan Afirka, da a wani lokaci aka mayar saniyar-ware wajen ayyukan noma, suna jagorancin yaƙi da tasirin sauyin yanayi, kuma suna bayar da gudunmawa wajen samar da abinci da kyautata jin-daɗin rayuwa.
women are often the first to notice environmental changes – and also the first to act. / Others
8 Mayu 2025

Daga Pauline Odhiambo

Filin noma mafi tsufa a duniya ya tsira saboda ‘yan adam sun koyi sabo, da sauya hanyar da suke mu’amalantar yanayi, da kuma ƙasa, da ma yanayin al’umma.

A yayin da sauyin yanayi yake keta tabbatattun hanyoyin rayuwa, tare da tursasa al’ummomin Afirka su sake tunanin yadda za su haɓaka tare da tsirar da kansu.

A yankin Maiduguri na Nijeriya, Hauwa Ibrahim, mahaifiyar yara shida ce mai shekaru 45. Ta yi zaton sun yi asarar komai bayan da ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da gonarta shekaru biyu da suka gabata.

Ba ta tsaya jiran tallafi ba, sai ta shiga ƙungiyar mata inda aka koya mata yadda za ta dinga shuka a cikin buhu - dabarar da ke barin ƙasa cikin laima ko da akwai ƙarancin ruwa.

“A baya muna yin shuka kamar yadda kakanninmu ke yi, duk da cewa ba a iya hasashen ruwan sama kamar lokutan baya. A lokacin da aka samu ambaliyar ruwa, wanda ana samu sosai, sai ruwan ya tafi da komai,” in ji Hauwa a zantawarta da TRT Afrika.

“Mun koma noman kayan miya a buhuna, da kiwon akuyoyi, da ajjiye kuɗaɗe a ƙungiyance. Mun tsira ne saboda muna aiki tare, da bin sabbin hanyoyi.”

Labarinta na bayyana halin da miliyoyin mata a Afirka ke ciki, waɗanda duk da sauyin yanayi ya shafe su, sun dage da bin sabbin hanyoyin neman mafita don kare iyalinsu da al’umunsu.

Cikin wata maƙalar aiki da ofishin Ci-gaba na Majalisar Ɗinkin Duniya ya buga a watan Afrilu, mawallafin, Samuel Hall ya ambato irin wannan gwagwarmaya - da kuma ƙananan nasarori - da ake gani a ayyukan da aka yi a Somalia, Kenya, da Nijeriya.

Fara ɗaukar mataki

Daga sauyawar saukar ruwan sama, zuwa ɓacewar burtalin kiwon dabbobi, rahotannin da ake samu na cewa mata ne ke fara gano sauyin yanayi - kuma su suke fara ɗaukar mataki.

A arewa maso-gabashin Kenya, Halima Adan, mai sana’ar kiwon dabbobi, ta tuna yadda fari ke ƙarar da dabbobin mutane, duk da cewa dabbobin su ne ababen tallafar rayuwarsu.

“Maza sun fita neman burtalin da dabbobi za su ci abinci, inda mu kuma muke zaune a gida da yara. Ba mu da madara, babu nama. Sai muka fara ƙananan sana’o’i, muna sayar da itatuwa da yin abin wuya. A yanzu muna da ƙungiyar tara kuɗaɗe don sayen irin da fari ba ya illatawa.” in ji ta.

Asha Ahmad, da ke shuka wake da masara a Tanzania, ta bayyana yadda mata a garinsu suka koma yin abin da ta kira “lambu a birane”.

“Muna amfani da tsaffin kwantena don shuka kayan miya. Ba mu da gonaki, amma haka muke yi. Matan na cewa noma aikin mata ne; a yanzu suna kallon sa a matsayin aikin adana kuɗaɗen mata,” in ji ta.

Dr Fatima Jibril, ƙwararriya kan sabo da yanayi wadda ke aiki da Cibiyar Manufofin Sauyin Yanayi ta Afirka, tana kallon wannan a matsayin samar da mafita ta yanzu.

“Abubuwan da matan nan ke yi da kwantenoni wajen yin lambuna, yana bayyana ɗaya daga hanyoyin magance illolin sauyin yanayi masu sauƙi da muka gani. Sabon abu ne da ke amfanar da miliyoyin mutane,” in ji ta.

Matsalolin zamantakewa

Duk da irin kayan arzikin da suke da shi, suna fuskantar cikas. Dokokin al’adu na takaita musu motsi da kai komo, cire su daga sha’anin kudi na takaita damarmakinsuna karbar bashi da daukar matakai.

“Mun san abinda jama’armu ke so, amma babu wanda yake tambayar mu,” Grace Muthoni, manomiya a Wadin Rift na Kenya, ta fada wa TRT Afrika. “A lokacin da Kungiyoyi suka zo, sun fi kula maza, amma mu ne muke yin shuka, debo ruwa da ciyar da yara. An yi biris da iliminmu.”

Sakamakon matsalar gonaki masu yabanya da suke fuskanta, mata sun samar da hanyoyin noma na basira. A Somalia, matan da aka raba da matsugunansu kamar Fadumo Hassan sun koma noma a buhuna da bokitai.

“Muna shuka amaranth da sukuma wiki a tsaffin jarkoki,” in ji Hassan daga Mogadishu. “SUna bukatar ruwa kadan kuma suna girma da wuri.”

Matan Kenya da Somaliya sun kudiri aniyar tara kudade wajen sayen irin da yake jurewa karancin ruwa da fari.

Dabaru na al’ada

Jama’a makiyaya sun koma kiwo kadan irin na awaki da ma kaji da ba sa bukatar ruwa da yawa.

“Bayan fari ya kashe shnu, sai muka sayo kaji,” in ji Naisiae Losokwan, wata mace ‘yar kabilar Maasai da jama’arta ke zaune ku sa iyakar Kenya da Tanzania. “Ba sa bukatar ruwa sosai, kuma muna da isasshen kwai na sayarwa.”

Farfesa James Kinyangi, babban mai bayar da shawara ga Bankin Duniya kan Sauyin Yanayi a Afirka, ya kira sauyi daga noman shanu zuwa na kaji a tsakanin mata makiyaya da “babban misalin sabawa da sabon yanayi”.

“Hakan na samar da abinci d arage dogaro a kan ruwa - wannan ne sauyin da muke son goyawa baya,” in ji shi.

Kungiyoyin mata a Nijeriya na amfani da hanyoyin gargajiya da na zamani wajen gargadin wuri. Kungiyoyin jama’a na sanar da lokacin ruwa o sanyi ta kafar rediyo da wayoyin hannu.

'“Kakata ta koya min karanta sama,” in ji Adong Florence, manomiya a Uganda. “A lokacin da wasu tsuntsaye suka yi sheka da wuri, mun san ruwa ba zai sauka ba.”

An shigar da wadannan dabaru cikin hanyoyin hasashen yanayi na kungiyoyi don samar da hasashe na gaskiya. 

Sauyawar al’adun jinsi

A yayin da sbaon da mata suke yi ya yi nasara, ana samun sabbin rawar da jinsi ke takawa. Mata matasa na samun horo kan noman zamani, inda maza ke karfafa musu.

“Mijina na cewa maza ne kawai ke kiwon dabbobi,” in ji Rukia Abdi, wata ‘yar kasar Kenya manomiya. “Amma ya sauya ra’ayinsa a lokacin da na fara noman kayan lambu da na ke ciyar da mu lokacin fari.”

A yayin da wannan yunkuri daga tushe ke bayyana juriya, matan da ke aiki wajen yaki da tasirin yanayi, na jaddada bukatar kayan aiki don magance matsalolinsu.

“Ba ma bukatar tausayi,” in ji Rukia. “Muna bukatar horo, basussuka, da wuri a teburan yanke hukunci. Ku ba mu kayan aiki; za mu yi mafi kyau.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us