Shekarar 2025 tana zamowa shekara mai cike da rikice-rikice, ciki har da wani sabon rikicin da ya ɓarke tsakanin kasashen duniya, amma fa ba rikicin tashin bama-bamai da harbe-harbe ba.
Rikici ne na tattalin arziki da gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta assasa, tsakaninta da ƙasashen duniya manya da ƙanana, ciki har da na Afirka irinsu Nijeriya.
Bari mu warware muku zare da abawa kan yadda wannan yaƙi zai shafi al’ummarmu da yadda za mu ji raɗaɗinsa.
Wannan abu ya kaɗa hantar gwamnatoci da hukumomi da ma al’ummar duniya daga Beijing zuwa Sydney, Johhanesbourg zuwa Alkahira, domin kuwa ba ƙaramin tasiri zai haifar ba kan tattalin arzikin kasashe da rayuwar al’ummominsu.
Sai dai shi Trump, ya kafa hujja ne da cewa ƙasashen duniya "sun daɗe suna ƙwarar ƙasarsa da kwashe arzikinta". Yana mai cewa “an kwashe shekaru fiye da 50 ana damfarar ‘yan ƙasa masu biyan haraji na Amurka," inda ya sha alwashin ganin hakan bai sake faruwa ba.
A farkon sanar da matakin, masana tattalin arziki sun yi hasashen cewa lamarin zai ta’azzara farashin wayoyi da komfutoci waɗanda mafi yawa a China ake ƙera su, inda za a samu ƙarin kashi 43 cikin 100 a kan farashin dukkan samfuran iPhone na yanzu.
Sai dai a ranar Asabar 12 ga watan Afrilu, Trump ya ce ya janye batun ƙarin harajin a kan wayoyi da komfuta, saboda a cewar Fadar White Houe, ana so a tabbatar da cewa kamfanonin da ke ƙera su sun samu isassehn lokacin mayar da cibiyoyinsu Amurka.
Mene ne harajin shige-da-fice?
Shi dai haraji da ake sakawa kayayyakin da ake shigarwa ko fitarwa daga kasa, wanda ake kira tariff, tamkar mashi ne mai baki biyu.
Kasa takan saka haraji ko kara haraji kan kayan da ake shigowa da shi cikin iyakokinta domin ta tara kudin shiga, wanda jami’an kwatam ke karba a kan iyakokin kasa.
Sannan kasa tana saka haraji kan kayayyakin waje don su yi tsadar idan an kwatanta su da kayayyakin da ake samarwa cikin gida, ko don a dakushe farin jinisu a kasuwanni, ko don martani kan kasar da ta saka haraji muku haraji kan kayayyakinku da ake kai wa can.
A yanzu yaƙin kasuwancin ya fi zafi ne tsakanin Amurka da China, wadda harajin da Amurka ta ƙaƙaba kan kayan da ake shigarwa Amurka daga China zai kai kashi 145 cikin 100.
Tuni ita ma Chinar ta ja tunga, ta ce duk wani nau’i na yaƙin kasuwanci da Amurka ke son ƙaddamarwa kanta, to a shirye take, ko-a-mutu-ko-a-yi-rai, inda ta mayar da martini wajen ƙaƙaba wa Amurka harajin kashi 84 cikin 100 kan kayayyakin Amurka da za a shigar ƙasarta.
A farkon sanar da matakin, masana tattalin arziki sun yi hasashen cewa lamarin zai ta’azzara farashin wayoyi da komfutoci waɗanda mafi yawa a China ake ƙera su, inda za a samu ƙarin kashi 43 cikin 100 a kan farashin dukkan samfuran iPhone na yanzu.
Sai dai a ranar Asabar 12 ga watan Afrilu, Trump ya ce ya janye batun ƙarin harajin a kan wayoyi da komfuta, saboda a cewar Fadar White Houe, ana so a tabbatar da cewa kamfanonin da ke ƙera su sun samu isassehn lokacin mayar da cibiyoyinsu Amurka.
Tasiri kan Nijeriya
Ita kuwa Nijeriya, wadda Trump ya ƙara mata harajin kashi 14 cikin 100, za ta fara ji a jikinta ne ta fannoni kamar faɗuwar farashin danyen man fetur a duniya da ma ƙara faɗuwar Naira.
Wani masanin tattalin arziki, Dokta Isa Abdullahi, malami a Jami’ar Tarayya ta Kashere a jihar Gombe ya shaida wa TRT Afrika cewa, tuni farashin gangar fetur ya fadi a kasuwannin duniya daga dala 75 ya koma dala 65.
Dr Isa ya ce hakan kuma na nufin kasafin kudin Nijeriya zai ji jiki kai-tsaye, saboda ya ta’allaƙa ne a kan farashin fetur, kuma an yi kasafin kudin kasar a kan farashin duk gangar mai ɗaya kan dala 75. Kenan ya zama wajibi ƙasar ta nemo yadda za ta cike giɓin da aka fara samu tun a yanzu.
Sai me kuma? Trump ya kassara dokar kasuwanci ta AGOA, wadda wani tsari ne da aka samar don taimaka wa ƙasashen Afirka su ribaci kasuwancin da Amurka ke yi a duniya.
Ita wannan doka na taimaka wa ƙasashe irin su Nijeriya sayar da kayayyakinsu na asali kamar kayan abinci irin su zogale da garin kwaki da ƙuli-ƙuli da sauran su, ba tare da an caje su haraji ba don su samu damar yin gogayya da sauran takwarorinsu na duniya.
Masanin tattalin arzikin, Dr Isa ya ce a yanzu da aka nakasta tsarin AGOA, to ɓangaren samun kuɗaɗen Nijeriya waɗanda ba na man fetur ba wanda a shekarun bayan nan yake bunƙasa sosai, a yanzu zai fuskanci cikas saboda yadda Trump ya soke dokar.
Sai kuma guguwar tsadar kayayyaki da duniya baki ɗaya za ta fuskanta, kuma kai-tsaye hakan zai fi shafar kasashen da ba sa samar da kayayyaki a cikin gida sai dai su shigo da su kamar dai Nijeriya.
Kana, akwai fargabar manyan kamfanonin duniya za su rage yawan abin da suke samarwa har ma da rage yawan ma’aikatansu, lamari mai matuƙar hatsari ga ɗan’adam.
Mafita ga ƙasashen duniya
Hanya ɗaya ta magance tasirin wannan mataki a Nijeriya, shi ne ƙasar ta dage ta fara amfani da ma’adanai da albarkatunta don samar da duk abubuwan da ake buƙata a cikin gida, har ma ta fitar da su kasuwannin duniya don riba, maimakon sayowa daga waje, in ji masana tattalin arzikin.
Wannan mataki na Trump da a yanzu ya jingine shi har tsawon kwana 90 kafin sake waiwayarsa, yana zuwa ne a lokacin da dama tuni duniya ta fara jin jiki ta fuskar tattalin arziki, sakamakon matsananciyar hauhawar farashi da tsadar rayuwa saboda tasirin da annobar korona ta yi a duniya.
Sannan kuma ga janye tallafin da Amurka ke bai wa ƙasashe masu tasowa a fadin duniya da shi Trump ɗin ya yi, jim kadan bayan rantsar da shi.
Duka waɗannan sun sa wasu na ganin sannu a hankali duniya na komawa turbar jari-hujja tsantsa, ta yadda ko amfani da shafukan sada zumunta da a baya yake kusan kyauta.
A yanzu kamfanonin suna ta tsaurarawa ta hanyar neman masu amfani da wasu fasalolin manhajarsu su biya kudi kafin samun damar amfana, kamar biyan kudi don samun alamar tantance a asusun sada-zumunta, da kuma tilasta wa kwastomomi sayen gurbin ajiya a manhajoji irinsu Google da iCloud.
Sai dai akwai masu sharhi kan siyasar duniya da ke cewa, shi Trump tamkar damisar takarda yake, don a yanzu ma bayan hargagin nasa, ya tsagaita wuta, sannan an jiyo shi yana cewa za su iya samun fahimtar juna shi da China, don warware wannan taƙaddama ta yaƙin kasuwanci.
Yanzu dai sai duniya ta zura ido don ganin yadda za a karke a wannan tataburza a dandalin cinikayya da kasuwancin duniya!