Ƙyama da camfi ne ke dagula matsalar cutar ƙyandar biri a Afirka
AFIRKA
5 minti karatu
Ƙyama da camfi ne ke dagula matsalar cutar ƙyandar biri a AfirkaƘyandar biri, da a baya ta kasance a wasu yankuna kawai, a yanzu ta mamaye nahiyar, tana yaduwa a lokacin da hukumomin lafiya ke rige-rige da lokaci wajen magance illarta ta hanyar riga-kafi da ƙarfafa wayar da kai.
Ana nuna kyama ga masu cutar mpox a wasu yankunan Afirka./ AA
2 Mayu 2025

Ta faro ne a matsayin wasu ‘yan kuraje a kirjin Joshua - babu wani abin damuwa, kamar dai yadda mahaifiyarsa Monique Baloji take tunani.

Ta fara zargin cewa Joshua na fuskantar borin jini ne kafin daga baya ta firgice bayan jikin yaron ɗan shekara uku ya kamu da ciwo sosai.

Jikin yaron ya kuma yi zafi matuƙa, yana ta kuka tare da ƙin cin abinci.

“Ban taba jin wani abu kan kyandar biri ba a baya,” Monique, ‘yar asalin yankin arewacin Kivu a Jumhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta fada wa TRT Afrika game da gano ciwon da ke damun danta. “A lokacin da muka je asibiti, jikin yarona ya yi rauni. A lokacin da likitoci suka ce ƙyandar biri ce, sai na ji kawai duniyata za ta rushe ne.”

A faɗin Afirka, ƙyandar biri ta tashi daga ‘yar ƙaramar cutar da ta yaɗu zuwa yankunan nahiyar da dama, ta yaɗu a sababbin yankuna tare a barin iyalai suna fama da raɗaɗinta.

Cibiyar Kula da Cututtuka Masu yaduwa da Riga-Kafi ta Afirka (Africa CDC) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun sabunta shirin yaƙi da cutar a nahiyar, inda suke ƙara ƙoƙari wajen shawo kan yaduwarta, tare da faɗaɗa allurar riga-kafi, da aiwatar da manufofin kula da lafiya na dogon zango.

Yaɗuwar cutar a faɗin nahiya

Tarihi ya nuna an fara daukan cutar daga dabbobin dake da ita, ɓarkewar ta a baya bayan nan ya sa an samu yaɗuwarta a tsakanin mutane. Cutar na janyo zazzabi, da kumburin fata da fesowar kuraje da jin kaikayi da ke janyo susa.

A 2022, wani nau’in cutar da ake kira “clade IIb” ya fara yaɗuwa a duniya, yawanci ana ɗaukar sa ta hanyar jima’i. Ya zuwa karshen 2023, sai mafi karfi ta ɓulla “clade Ib”. wadda ba ta hanyar jima’i kaɗai ake ɗaukar ta ba, har ma ta hanyar mu’amalar cikin gida.

A watan Agustan bara, Hukuma CDC ta sanar da Dokar ta Ɓaci bayan ta biyun ta ɓulla tare da yauɗwa a wasu ƙasashen.

Tun wannan lokacin, ƙasashen duniya 28 sun bayar da sanarwar ɓullar cutar, inda Afirka ta fi ko’ina yawan masu ɗauke da cutar da yin kisa.

A wajen Afirka, mafi yawan kamuwa da cutar na da alaƙa da tafiye-tafiye. A cikin nahiyar, an samu daɗuwar yaduwar cutar a tsakanin mutane, inda har ta kai ga Tanzania da Zambia, da a baya babu masu ɗauke da cutar.

Yada bayanan karya

A Nairobi, matashiyar uwa ta kamu da ƙyandar biri daga mijinta, direban babbar mota da ke zuwa ƙasashen Gabashin Afirka.

“Da fari, maƙota sun guje mu. Sun yi tunanin tsine mana aka yi. Har dangi ma sun daina ziyartar mu,” in ji matar ‘yar Kenya mai shekaru 32 a yayin tattaunawa da TRT Afrika.

Frank Lubega, ɗalibin jami’a a Uganda, har yanzu yana tuna wahalar jiki da ta kwakwalwa ta cutar kyandar biri.

“Tsawon makonni, ba na iya kallon madubi,” in ji shi. “Mafi muni ba wai zafin ba ne - shi ne yadda mutane ke kallo na.”

Dr Fanuel Odongo, jami’in lafiya a Kenya, ya ɗora laifin kan yaɗa bayanan ƙarya kan matsalar ƙyandar biri.

“Mutane na ɓoye nasu alamun saboda suna tsoron kar a nisance su. Wannan kuma na sanya cutar ta yi ta yaɗuwa ne,” kamar yanda ya yi gargaɗi.

Riga-kafi da sanya idanu

A lardin Copperbelt na Zambia, Vanessa Musonda na kula da mijinta da cutar ta kama a lokacin da take kokarin kare yaranta daga kamuwa.

“Muna kwana a dakuna daban-daban, amma na ɗimauta saboda tunanin yaranmu za su kamu da cutar,” ta faɗa wa TRT Afrika. “Har yanzu babu allurar riga-kafi a nan. Muna addu’a ne kawai.”

Duk da cewa ana kan gangamin alluran riga-kafi, inda aka rarraba ƙwaya 650,000 a ƙasashen Afirka shida, (kashi 90 a Kongo), ana buƙatar ƙari da yawa - cikin hanzari.

Dr Jean Kaseya, jajirtaccen jami’in kula da lafiya a yankin Goma na Kongo, ya bayyana yaki da ƙyandar biri a matsayin wani gagarumin aiki fiye yaki da wata mastsalar lafiyar al’umma.

“Muna yin alluran riga-kafin cikin sauri, amma ƙyamar da ake nuna wa ƙyandar biri a gabashin Kongo na tattare da dukkan jama’ar. Mutane na tsoro, kuma wasu sun yi imanin cewa ƙyandar biri la’anta ce,” in ji shi.

A ɓangare mafi kyau kuma,ɗakunan bincike da gwajin lafiya a DRC sun ƙaru sosai, inda ake da ɗakunan gwaji 23 - daga ƙwaya biyu kawai da ake da su a 2023.

Ɗorewar wannan abu ya dogara kan yadda cikin hanzari mahukunta suka kawar da gibin kashe kudade da ke yin barazana, domin har yanzu ana buƙatar sama da dalar Amurka miliyan 220.

Neman mafita

A yayin da CDC ta Afirka da WHO suke ta bayyana dabarun yaki da ƙyandar biri, iyalai irin su Monique na jiran ganin lokacin da cutar za ta zama ta daina barazana ga lafiyar yara.

Bayan fama da ƙyandar biri da Joshua ya yi, Monique ta tsorata sosai. Keɓe kai na makonni da kula da lafiya a kan kari sun kuɓutar da rayuwar yaron, amma tabon na nan - na jiki da ƙwaƙwalwa.

“Bai kamata wani yaro ya faɗa wannan matsala ba,” in ji ta, tana ɗauke da yaronta a tsumman goyo. “Muna buƙatar taimako a yanzu, kuma dole ne shugabanninmu su ɗauki matakin kawo ƙarin alluran riga-kafi, da ɗaukar matakin ƙarin wayar da kai.”

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us