Yayin da ya rage shekaru biyu kafin gudanar da babban zaɓe a Nijeriya, jam’iyya mai mulkin ƙasar tana samun nasarar amsar gwamnonin jihohi, da ‘yan majalisun ƙasa, da manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyun adawa.
Lamarin ya kai ga masu lura da harkokin siyasar ƙasar sun fara nuna fargabar cewa Nijeriya ta kama hanyar komawa ƙasa mai jam’iyya guda.
Zuwa ƙarshen Afrilun 2025, jam’iyyar All Progressives Party, APC na riƙe da shugabancin ƙasa, da majalisun dokoki biyu na ƙasar, da kuma rinjayen yawan gwamnoni da jagorancin majalisun dokoki, da na ƙananan hukomomi.
Cikin jihohi 36 na ƙasar, APC tana da gwamnoni 22, sai Peoples Democratic Party (PDP) mai gwamnoni 11, sai All Progressives Grand Alliance (APGA), da Labour Party, da New Nigeria Peoples Party (NNPP) masu gwamnoni guda-guda.
Cikin wata guda, APC ta karɓe gwamnan jihar Delta da ke kudu maso kudancin ƙasar, Sheriff Oborevwori, wanda ya ci zaɓe ƙarƙashin PDP, da kuma ’yan majalisar dokokin jihar da ta kasance a hannun PDP tun 1999.
Baya ga gwamnan jihar ta Delta, APC ta yi babban kamun tsohon gwamnan Delta, wanda kuma shi ne ya yi wa PDP takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa, tare da sauran muƙarraban PDP a jihar.
‘Dalilan’ sauya sheƙa
Tsohon gwamna Ifeanyi Okowa ya yi jawabi kan dalilan sauya sheƙarsu a birnin Asaba ranar Litinin 28 ga Afrilu, yayin da shugabannin jam’iyyar APC suka yi bikin karɓar su.
Ya ce, “Mutane na mamakin me ya sa, amma abu guda na da muhimmanci: a tarihin al’umma a kullum akwai lokacin sauyin tafarki don kyautata rayuwar al’umma, kuma duk matakin da muka ɗauka kan wannan turba ne da kuma kyautata jiharmu”.
Okowa ya jaddada cewa sauyin ya wajaba domin jihar Delta ta iya inganta alaƙarta da gwamnatin tarayya, da kuma samun alfanu daga albarkatu da damarmakin da ke hannun gwamnatin tarayya da ke Abuja.
Baya ga jam’iyyar PDP, guguwar sauya sheƙa zuwa APC ta damƙo wasu jiga-jigan jami’iyyar adawa ta NNPP. Ranar 24 ga Afrilu, wasu manyan ‘yan siyasar jihar Kano da ke arewa maso yammacin ƙasar sun fita daga jam’iyyar.
Ko da dai ba a kai ga karɓarsu a jam’iyyar APC ba, amma a baya bayan nan ana ganinsu suna yin taro da shugabannin APC, ciki har da shugaban jam’iyyar na ƙasa Umar Abdullahi Ganduje
Masu riƙe da muƙamai da wasu ‘yan siyara na jam’iyyar NNPP da suke shirin shiga APC sun haɗa da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar shiyyar Kano ta Kudu, da wasu ’yan majalisar wakilai na yankunan jihar Kano.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce akwai wasu ƙarin gwamnoni na jam’iyyun adawa da za su shiga jam’iyyar APC a nan gaba kaɗan.
Zargin ƙarfa-ƙarfar APC
Yin ƙaura zuwa jam’iyya mai mulki abu ne da ke tayar da hankalin ‘yan siyasa da magoya bayan jam’iyyun hamayya, inda waɗansunsu ke zargin akwai maƙarƙashiya da APC mai mulki ke shirya wa jam’iyyun adawar ƙasar gabanin zaɓe mai zuwa.
Wani jagoran ’yan adawa a Nijeriya kuma ɗan takarar shugabancin Nijeriya a PDP a zaɓen 2023 Atiku Abubakar, ya ce dimukuraɗiyya ta bai wa kowa ’yancin kasancewa a tafiyar da ya zaɓa da kuma ’yancin faɗin albarkacin baki.
Sai dai akwai masu ganin jam’iyyar APC da gwamnatin tarayyar Nijeriya na amfani da cin-hanci, da romon baka ga ‘yan adawa, da tayin muƙamai, da kuma hukumomin gwamnati, da ma wasu alƙawuran alfanun da suka danganci siyasa da tattalin arziƙi.
Shi ma wani jigo a PDP kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana ficewar da ake yi daga PDP a matsayin wani babban haɗari da ke tunkarar siyasar Nijeriya.
Ya yi zargin cewa gwamnatin APC ce take yi wa PDP bita-da-ƙulli, kamar yadda shi ma wani ɗan adawa, Dele Momodu, mawallafin mujallar Ovation, ya zargi jam’iyya mai mulki da tursasa wa mutane shiga cikinta.
Martanin jami’yyar APC
Fadar gwamnatin Nijeriya ta yi martani kan masu sukar yadda ‘yan siyasa ke tururuwar shiga jam’iyya mai mulki ta APC.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya ce zarge-zargen Tinubu yana ƙoƙarin assasa mulkin jam’iyya guda “zance ne mara tushe da ake zuzutawa”.
Onanuga ya ce fadar gwamnatin ba ta da wani shiri na raunata jam’iyyun hamayya kamar yadda wasu ke iƙirari.
Ya kuma soki masu wannan zargi kan cewa ba su yi wannan suka ba lokacin da wasu ‘yan siyasa suka fara kafa gamayya don kawar da APC a zaɓen 2027, inda ya ba da misali da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da ya bar APC zuwa SDP.
Ya ƙara da cewa babu ƙarfa-ƙarfa a harkar, kuma dimokuraɗiyya ba ta cikin haɗari a Nijeriya, domin kuwa ‘yan siyasa suna bin ‘yancinsu ne da shiga duk wata jam’iyya da suka zaɓa.
Me ne haɗarin mulkin jam’iyya ɗaya?
Wasu masana siyasar Nijeriya suna kallon yawaitar sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki a matsayin abu mai barazanar mayar da Nijeriya ƙasa mai jam'iyya ɗaya, abin da wasu ke ganin cikas ne ga tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.
Farfesa Kamilu Sani Fagge na Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano a Nijeriya, ya shaida wa TRT Hausa cewa ana yawan sauye-sauyen sheƙa ne saboda ba a gina siyasar ƙasar kan aƙidu ko manufofi ba.
Ya ƙara da cewa an gina siyasar ne kan biyan buƙatar ƙashin-kai, wanda ya sa ’yan siyasar ke fita daga wannan jam’iyya zuwa wata, da zarar buƙatunsu ba su biya ba.
Malamin jami’ar ya ce ko da ƙasar ba ta koma tsarin jam’iyya guda ba, to shakka babu ta kama hanyar komawa tsarin danniyar jam’iyya ɗaya, wanda zai mayar da jam’iyya ɗaya ta zama mai ƙarfi sosai ta yadda jam’iyyun adawa za su rasa tasiri.
Baya ga barazana ga siyasar adawa, masanin ya ce ita kanta jam’iyyar da ake tururuwa cikinta za ta iya fuskantar rikicin cikin gida, saboda kowa ya tare a cikinta, ta yadda za a samu rashin wanyewa lafiya.
A fili take, babban ƙalubalen rashin masu adawa da gwamnati mai mulki shi ne haɗarin shugabancin kama-karya, ta yadda masu mulki za su riƙa yin abin da suka ga dama, ba tare da jin tsoron ’yan adawa ko faɗuwa zaɓe ba.