Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bi sahun kasashe da dama wajen kakaba takunkumi kan shafin shahararren gem din Roblox na Amurka, saboda damuwar da ake ita ta kare yara kanana.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Anadolu, takunkumai da matakan da aka dauka a kasashen gabar Tekun Fasha sun bambanta sosai - daga takaita amfani da gem din zuwa dakatar a wani bangare nasa da ma dakatar da shi na wucin gadi, har sai an kammala nazari kan damuwar da ake da ita.
Manhajar gem din, wanda ke ba masu amfani damar tsarawa da yada nasu wasannin tare da wasu, ya samu habaka mai ban mamaki a cikin 'yan shekarun nan, sau da yawa ma ga yara kanana da ke manne da gem-gem da sunaye irin su Tower of Hello.
Amma Roblox ya fada komar bincike yayin da yawancin iyaye ke yada bidiyon wasu manyan mutane da ke zuwa kofar gidajensu da haduwa da yaransu bayan sun zama abokai da su a manhajar gem din.
Matakan Saudiyya
Tashar talabijin ta Al-Ekhbariya ta Saudiyya ta bayar da rahoto a ranar Alhamis cewa, Babbar Hukumar Kula da Kafafen Sadarwa Kallo da Sauraro ta umarci Roblox da ya cire tsarin yin magana da murya da rubutu da kuma da kuma inganta sa ido kan abubuwan da ke ciki.
Hattan Tawaili, shugaban Sashen Wasannin Gem na hukumar, ya ce dakatar da tsarin aika sakonni wani mataki ne na wucin gadi "don inganta wa da haɓaka dokokin kula da gem din, tare da tabbatar da yanayin kare masu amfani da ma yanayin amfanin.
Roblox ya tabbatar a cikin wata sanarwa da kafofin yada labarai na Saudiyya suka fitar cewa "ya himmatu wajen biyan bukatun Babbar Hukumar Kula da Kafafan Sadarwa na Sauraro da Kallo game da sanya idanu kan gem din da magance cin zarafin yara.
Kamfanin ya kara da cewa, bayan tattaunawa da hukumomin Saudiyya da dama, ya yi alkawarin "habaka wa tare da inganta karfinmu a fannin sadarwa da harshen Larabci da daidaita abubuwan da gem din ke dauke da su."
Wani rahoto da aka fitar a shekarar 2024 na Hukumar Sadarwa, Sararin Samaniya da Fasaha ya bayyana cewa Roblox ya zama na biyu mafi yawan saukarwa a tsakanin gem-gem a na’urorin masu amfani a masarautar.
Matsayin Hadaddiyar Daular Larabawa
A Hadaddiyar Daular Larabawa, Hukumar Sadarwa da Hukumar Kula da Fasahar Digital ta Gwamnati sun sanar a ranar Alhamis cewa an gabatar da sabbin gyare-gyare tare da haɗin gwiwar Roblox don haɓaka amincin dijital ga masu amfani, musamman ma yara kanana.
Sauye-Sauyen sun haɗa da "Rufe aikin wasu fasalolin sadarwa na ɗan lokaci, kamar aika sako a yayin da ake yin gem, a matsayin wani ɓangare na matakan riga-kafi don kare matasa masu karancin shekaru," a cewar sanarwar.
Gyare-Gyaren kuma sun haɗa da haɓaka daidaita abubuwan da ke a harshen Larabci, haɓaka abubuwan da iyaye za su sanya idanu a kai, da gabatar da sabbin tsare-tsaren kariya.
An toshe hanyoyin ganin Roblox a wani wajen
Hukumar Kula da Sadarwa da Fasahar Sadarwa ta Kuwait ta fada a cikin wata sanarwa a ranar 21 ga Agusta cewa ta toshe hanyoyin amfani da Roblox a fadin kasar.
Matakin ya samo asali ne daga hurumin hukumar bisa doka na kare masu amfani, musamman ma yara, a yayin da korafe korafe daga iyaye da jami'ai game da "abubuwa marasa kyau, cin zarafi a lokacin amfani da yanar gizo, halaye masu cutarwa, da kuma abubuwan da ba su dace ba da kuma hanyoyin sayayya marasa tsaro."
Hukumar ta jaddada cewa dakatarwar ta wucin gadi ce har sai an kammala tattaunawa da kamfanin, kuma har sai Roblox ya cire abubuwan da ke da illa da kuma tabbatar da isasshiyar kariya ga yara.
A ranar 13 ga Agusta, Qatar ta kuma dakatar da Roblox "don kiyaye dabi’un yara da matasa," a cewar kafofin watsa labarai na cikin gida, ciki har da Al Jazeera.
A watan Yuni, jami'in kula da harkokin sadarwa na Oman ya tabbatar wa jaridar Atheer ta kasar cewa a hukumance an haramta Roblox a fadin kasar.
An haramta shi a Turkiyya
A ranar 7 ga watan Agusta wata kotu a kasar Turkiyya ta toshe manhajar wasannin gem ta yanar gizo, saboda nuna damuwa kan abubuwan da ka iya haifar da cin zarafin yara.
Ministan shari'a Yilmaz Tunc ya bayyana ta shafin X cewa "Ya zama tilas kasarmu ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron 'ya'yanmu."
Ya ce wata kotun Turkiyya ta hana shiga wasan bayan wani bincike da masu gabatar da kara suka gudanar a lardin Adana da ke kudancin kasar, wanda ya samo asali daga nuna damuwa kan yadda ake amfani da manhajar wajen cin zarafin yara.
Gem din na shan suka
A watan da ya gabata, jihar Louisiana ta Amurka ta shigar da kara kan Roblox, inda ta zargi kamfanin da taimakawa wajen cin zarafin yara.
Roblox ya yi watsi da zargin a matsayin "karya," a cewar BBC.
Roblox kyauta ne, gem da ke da dadi da hira da juna da aka kirkira kusan shekaru 20 da suka gabata.
Babban tsarin gem din na baiwa masu amfani damar "tsara nasu duniyoyin kamar a mafarki" tare da kayan shirye-shirye masu sauƙi, fita ga zaga yankuna, yin wasa da wasu tare, da yin mu’amala a kan iyakokinsu.
Gem din ya jawo hankalin masu amfani kusan miliyan 85, kashi 40 cikin 100 na wadanda ba su kai shekaru 13 ba, a cewar rahoton watan Mayu na jaridar Guardian ta Birtaniya.
A shekarar 2023 kadai, an samu fiye da cin zarafn yara 13,000 a manhajar Roblox a Amurka, tare da mika wa mahukunta korafi sau 1,200 game da Roblox kan matsalolin cin zarafi.
Wata kafar yada labaran harkokin kudi ta Amurka Bloomberg ta ruwaito a 2024 cewa 'yan sandan Amurka sun kama akalla mutane 24 tun daga shekarar 2018 bisa zargin satar mutane ko cin zarafin mutanen da suka hadu da su ko kuma suka yaudare su ta hanyar Roblox.
A watan Agusta kamfanin ya kuma ce matsakaitan masu amfani da shi na yau da kullun sun kai miliyan 111.8, kuma sun aika sakonnin hira biliyan 6.1 tare da loda abubuwan da suka ƙirƙira a kan manhajar.
Kasuwar gem din bidiyo ta duniya tana ci gaba da faɗaɗa cikin sauri, tare da fiye masu amfani biliyan 3.4, kuma an yi ƙiyasin darajar kasuwar ta kai dala biliyan 200, kamar yadda alkaluman da na hukuma ba suka bayyana a 2024.