Daga Yahya Habil
A wani zaman jin ra’ayin jama’a na Kwamitin Ayyukan Soji na Majalisar Dattawan Amurka, Michael Langley, shugaban Sansanin Amurka a Afirka (AFRICOM) kuma Kwamandan Dakarun Ruwan Amrka, ya zargi Shugaban Rikon Kwarya na Burkina Faso, Ibrahim Traore da tsagwaron cin hanci da rashawa, yana mai cewa “Duk arzikin zinaren Burkina Faso zai dinga bayar da kariya ga gwamnatin sojin ne.”
Wannan zargi ya janyo mayar da martani daga al’ummun Afirka a duniya, musamman a tsakanin ‘yan kishin Afirka, wadanda cikin hanzari suka je yanar gizo suna bayyana rashin jin dadinsu.
Ibrahim Traore da shugabannin makotansu Mali da Nijar - Assimi Goita da Abdourahamane Tchiane - sun kasance shugabannin kasashen Afirka da a yau suke gwagwarmayar adawa da mulkin danniyar Yammacin duniya inda tuni suka kafa Kawancen Kasashen Sahel (AES).
Magoya bayan Traore, sun kalli zargin jaral din na Amurka a matsayin takalar fada ga kawancen, wanda suke yi wa kallon tubalin tsaywar Afirka da kafafunta wajen kalubaantar karfin Yammacin duniya.
Babban abinda ke sanya ‘yan Afirka a duniya ke goyon bayan Traore shi ne kalubalantar ‘yan mulkin danniya da kishin Afirka da yake yi.
Madadin Yammacin duniya
A matsayin dan juyin juya hali kuma mai kishin Afirka, Shugaba Ibrahim Traore na Burkina Faso ya samu karin shuhura a wajen ‘yan Afirka a duniya ind ake yi wa hawan s amulki a matsayin matakin da zai raba kasar ta Sahel daga zaluncin Faransa.
Faransa da kasashen Yamma sun ga yadda suka rasa dama a Burkina Faso da ma sauran yankin Sahel a matsayin babban kutufo ga ayyukansu na kasa da kasa a yankin.
Wannan na zuwa ne saboda raguwar karfin fada a jin Yammacin duniya a Sahel na nufin fadadar karfin fada a jin Rasha, inda a yanzi ita ce babbawa abokiyar adawar Yammacin duniya a Afirka.
Wannan shaida ce a ke bayyana karfafar alakar Rasha da kasashen yankin Sahel, wanda a baya bayan nan ma aka ga Traore ya baiwa kamfanin rasha na “Nordgold” lasisin hako zinare a kasar.
Wani karin bakin cikin ma ga Yammacin duniya, ba rasha ce kadai ke kara karfafa alaka da kasashen Sahel ba, Turkiyya ma na kara dasa kanta da smaun karfin fada a ji a Sahel.
Kamar dai yadda Rasha ta yi, Turkiyya ma ta sanya hannu kan yarjejejniyar hakar ma’adanai da Nijar a watan Oktoban bara.
Wannan ci gaba ya zama mummunan labari ga Yammacin duniya inda Turkiyya ta shiga tsama da Faransa saboda ayyukanta a Afirka, kuma kamar yadda aka sani Faransa na wakiltar bukatun kasashen Yamma a yankin Sahel.
Saboda haka, tabbas mahukuntan kasashen Yamma za su hari kasashen Sahel, Traore da kokarinsa na fitar da gwala-gwalai.
‘Yan kishin Afirka sun san wannan sosai, kuma wannan ne ya janyo suke mayar da matrtani kan zargin na Langley, inda suke tunanin lallai kasashen Yamma za su iya kokarin sake kafa karfin ikonsu a yankin Sahel kuma za su iya yin duk mai yiwuwa don halasta mamayar yankin.
Wannan mataki ba bakon abu ba ne a dabarun Yammacin duniya da Amurka na cim ma manufofi a kasashen waje, kamar yadda a baya muka gani bayan yin irin wadannan zarge-zarge da suka ingiza Amurka shiga wasu yankuna na duniya inda bukatun Yamman suka shiga hatsari.
Manufofin kishin kasa na Traore
Babban misalin da za a iya bayarwa shi ne na afkawa Iraki da Amurka ta yi, inda suka ce Iraki na habaka makaman kare dangi, amma fa ba hakan ba ne, kawai dai saboda Iraki na kawo cikas ga cim ma manufofin Yammacin duniya a Gabas ta Tsakiya.
Saboda haka, za a iya kawo makamancin hakan tsakanin batun Iraki da na Burkina Faso. A bayyane take karara cewa Yammacin duniya ba sa shiri da ‘yan kishin kasa da ke kalubalantar mamayar Yamma, ko a kasashen Larabawa, ko a Afirka.
Traore na Burkina Faso ya zama babban abin misalin hakan, kamar yadda aka ga ana dabbaka manufofin kishin kasa a kasarsa.
Mislai, kasar ta baiwa ‘yan kasa kawia izinin hakar gwala-gwalai a Boungou da Wahgnion.
A bayyane sosai ma, an yi watsi da Faransansanci a matsayin yaren hukuma na kasar, haka ma an haramtawa ma’aikatan gwamnati dalauyoyi saka tufafin Yammacin duniya, inda suke saka na al’ada a kasar.
A wajen ‘yan Afirka da ke sassan duniya daban-daban, wadannan matakan na nufin shakar sabuwar iska. A wajen ‘yan Afirka da dama, Traore na wakiltar matasa a doron shugabanci a Afirka, kuma sbauwar fuskar shugabanci da za ta iya kawo karshen karfin fada a jin Yammacin duniya a Afirka.
Son kai da munafurcin Yammacin duniya
A gefe guda, ya kamata Yammacin duniya su daina nuna kamar su ne masu kare dimokuradiyya a duniya, saboda su kan su sun bar manyan jigogin dimokuradiyyar.
Bayan komawarta tsarin fito da bukatun jama’a da ‘yan tsiraru masu kudi su dinga shugabanci, gwamnatin Amurka ta yanzu ma ba ta da wasu darajojin dimokuradiyya.
‘Yan Afirka sun shaida gwamnatocin Amurka da manufofinsu na siyasa a baya. Sun ga irin hanyoyin da suka bi bi wajen nufar kasashen Afirka da ba s abiyan bukatun kasashen Yamma.
A yanzu sun fahimci cewa mahukuntan kasashen Yamma ba su damu da walwala ko jin dadin kasashen Afirka da ma halayyar shugabannin kasashen ba, kawai suna kallon ko shugabannin na biyan bukatunsu ne ko akasin haka.
A wani kaulin kuma, ‘yan Afirka sun sani sarai cewa Yammacin duniya za su rufe idanunsu daga shugabanni masu aikata cin hanci da rashawa matukar dai suna biya musu bukatunsu.
Wannan ne dalilin da ya sanya ‘yan Afirka a yanzu ba sa damuwa saboda an bijirewa kasashen Yamma.
Marubuci Yahya Habil, dan jarida mai zaman kansa ne da ke Libya da ya mayar da hankali kan harkokin Afirka.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.