Mataki mafi tsanani na ciwon kwakwalwar Samuel Kiprono ya zo ne a wata tsakar rana a birnin Nairobi a loakcin da ya furta tunanin kashe kansa ga wand ya amince da shi sama da kowa - malaminsa na coci.
Amma maimakon a tausaya masa, sai ya gamu da suka d akushewa masu razanarwa.
“Ya fada min cewa ba damuwa ce ke damuna ba, shaidanu ne. Mun yi addu’a tare sannan ya ba ni wasu takardu na karanta, wadanda sun dan yi amfani. Duk da niyyarsa na da kyau sosai, amma ciwon damuwata ya ci gaba,”akawu mai shekaru 28 ta fada wa TRT Afrika,
Abinda ya fuskanta na wakiltar irin halin da masu wannan cuta ke ciki a Afirka.
‘Shan wahala a sirrance’
A yankunan Afirka, hudu daga cikin mutum biyar da ke fama da ciwon kwakwalwa ba sa samun kulawa - gibin da ke barin iyalai da dama a cikin mummunan yanayin rayuwa.
Ciwon kwakwalwata ya mayar da ni wani snaiyar war,” in Fatoumata Diallo mai shekaru 26, wata mai sana’ar yankan farce a Dakar. “Suna kira na da ‘mace mahaukaciya’ suna boye ni daga maziyarta. Asibitin na ba ni kwayoyi guda biyu ne kawai, babu wani abu kuma na kulawa, ba mutuntawa.”
Mafi yawan ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa a Afirka na karbar kudade kai tsaye daga makusantan marasa lafiyan. Ga wadanda ba su da kudi d yawa ko masu rauni, wadannan kudade na iya janyo musu wahalhalu sosai.
Amma Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kawo agaji ga wadanda ke shan wahala a sirrance ta kaddamar da sabon tsarin kula da masu ciwon kwakwalwa a fadin nahiyar.
Salon kulawar WHO
Sabon shirin na WHO na fuskantar wannan rashin nasara kai tsaye, yana mai kira ga yin sauye-sauyen gaggawa.
Shirin da aka kaddamar a ranar 25 ga Maris din 2025, na bukatar kawo karshen zagi da kyarar da ake nuna wa masu wannan cuta tare da daina takura musu su kebe kawunansu.
Maimakon wadancan munanan hanyoyi, shirin ya kawo tsarin nuna tausayawa, kulawa a cikin al’umma da ta maye gurbin tsohuwar kulawa
Wani abu mai muhimmanci, shirin na bukatar a samar da zuba jari a ayyukan kula da lafiyar kwakwalwa da tabbatar da horar da ma’aikata, tare da samar da tsarin abibiti mai rahusa a tsakanin al’ummu.
A yayin da shirin yake a bayyane yake karara, kalubalen na ci gaba.
Kasashen Afirka da dama na kashe kasa da kashi 1 na kasafin kudin kula da lafiya kan lafiyar kwakwalwa.
Amma Dr. Michelle Funk, shugabar manufar yaki da cutar kwakwalwa ta WHO ta nace kan cewar akwai yiwuwar a samu cigaba. “Wannan ba batun kudi ba ne kawai - batu ne niyyar ‘yan siyasa mai kyau da gyara mai kyau.”
Wani abu shi m ada ke da muhimmanci a sabon shirin shi ne wadanda suka kubuta daga cutar su zama suna da ruwa da tsaki a duk wani yunkuri na taimakon rayuwarsu
“Abin da ya kubutar da ni ba magani ba ne kawai, har ma da samun mutanen da suka fahimci lamarin,” in ji ta.
“Ma’aikatan sun koya min cewa ba saniyar ware ba ce ko wata tsinanniya - rashin lafiya na ke yi, kuma za a iya warkewa. A yau, ina jagorantar kungiyar da ke taimaka wa wasu wajen warkewa.”
Kula da ɗan’adam
Da yawa da kwararru kan cutar kwakwalwa da sauran kwararru a Afirka sun yi maraba da wannan sabon tsarin na WHO.
“A tsawon zamaninnika, mun yi maganin cututtukan kwakwalwa a matsayin maita ko rauni. Ba zan iya tun adadin mutum nawa muka yi wa magani da aka dinga nuna wa ƙyama saboda wannan,” in ji Dr. Amina Abubakar, wata likitan mahaukata da ke Legas.
“Wannan tsari na WHO na ba mu damar yadda za mu gina dan adam, tsarin da ke hakurtar da marasa lafiya da sanyaya zukatansu, maimakon guje musu.”
Malaman addini na zamani ma a yau na aiki don kawar da wannan mummunar fahimta game da ciwon kwakwalwa.
Wannan sauyi na zuwa ne a yayin da WHO ta yi gargadi game da rikicin ciwon kwakwalwa a Afirka da ke kara munana, amma kuma wasu al’adu suke kara ta’azzara su.
Wasu kungiyoyin addini a Afirka na hada kai da kwararrun kula da lafiyar kwakwalwa wajen taimaka wa masu fama da ita.
“Kubutar da rayuka ne abu mafi tsarki. A matsayin malamin addini, dole ne mu fahimci lokacin da ba addu’a kadai mutane ke bukata ba,” Pastor Joseph Mugisha, wanda ke jagorantar wata coci a Uganda ya fada wa TRT Afrika.
“Waraka na iya zama ta magani ko addu’a, amma idan mutum ya ce yana son ya mutu, to wannan bukatar magani ta gaggawa ce da ya kamata a yi.”
Ga wadanda suka kubuta irin su Samuel, wadannan sauye-sauye sun zo a makare amma na sanya fata nagari ga wasu.
“Watakila yanzu,” ya fada a ciki-ciki, “a lokacin da wani ya ce yana shan wahala, za su samu addu’a da taimakon da ya dace.”